Yanzu-yanzu: Kotu ta baiwa tsohon Antoni Janar, Mohammed Adoke, belin N50m

Yanzu-yanzu: Kotu ta baiwa tsohon Antoni Janar, Mohammed Adoke, belin N50m

Wata babbar kotun birnin tarayya dake zamanta a Gwagwalada ta baiwa tsohon Antoni Janar na zamanin Jonathan, Mohammed Adoke, belin N50m.

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da Adoke ne tare da shugaban kamfanin man Malabu oil and Gas Limited, Aliyu Abubakar, da Rasky Gbinigie, na kamfanin Agip, kan laifuka 42 na rub da ciki da babakere.

EFCC ta yi zargin cewa Adoke ya amshi cin hancin N300 million daga hannun Aliyu kan rijiyar man OPL 245.

Adoke ya musanta dukkan zarge-zargen 42 da ake masa gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel