Kisan Sojoji a Delta: Abubuwan Sani 5 Dangane da Jana'izar da Za a Yi Wa Jami'an Tsaron

Kisan Sojoji a Delta: Abubuwan Sani 5 Dangane da Jana'izar da Za a Yi Wa Jami'an Tsaron

  • Sojojin da aka yi wa kisan gilla a jihar Delta za a sada su da makwancinsu na gaskiya a ranar Laraba, 27 ga watan Maris 2024
  • Kakakin rundunar sojojin Najeriya, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ne ya tabbatar da hakan a cikin watan sanarwa
  • Sojojin 17 da aka kashe za a karrama su da lambar yabo ta ƙasa a yayin jana'izarsu a maƙabartar ƙasa da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An shirya bikin binne jami'an sojoji 17 da aka kashe a yankin Okuama na jihar Delta a ranar Laraba 27 ga watan Maris, 2024.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana hakan a wata sanarwa a shafin X ranar Talata, 26 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun shiga daji sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a Katsina

Sojojin da aka kashe a Delta
Za a gudanar da jana'izar sojojin da aka kashe a Delta ranar Laraba Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Jami'an sojojin dai sun rasa ransu ne bayan wasu ƴan bindiga sun yi musu kwanton ɓauna, bayan sun je kwantar da tarzoma a tsakanin al'ummar Okuama da Okoloba masu rikici da juna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kisan sojojin dai ya girgiza ƙasar nan sosai, inda aka shiga jimami tare da Allah wadai da wannan ɗanyen aikin da aka aikata.

Rundunar sojojin Najeriya ta sha alwashin zaƙulo waɗanda suka aikata laifin domin fuskantar hukuncin da ya dace da su.

A nasa ɓangaren, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya umurci jami'an tsaro da su tabbatar sun cafko masu hannu a kisan gillan tare da hukunta su.

Abubuwan sani dangane da jana'izar sojojin

Jaridar The Nation ta tattaro muhimmin abubuwa biyar dangane da jana'izar sojojin da za a gudanar a yau Laraba, 27 ga watan Maris 2024.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai halarci jana'izar sojojin da aka kashe a Delta, bayanai sun fito

Ga jerinsu nan ƙasa:

  • Za a yi jana'izar ne a maƙabartar ƙasa da ke birnin tarayya Abuja
  • Za a yi jana'izar sojojin ne da misalin ƙarfe 3:00 na rana
  • Shugaba Bola Tinubu ne zai kasance babban baƙo na musamman a wajen jana'izar
  • Za a karrama sojojin da aka kashe da lambar yabo ta ƙasa
  • Sojoji sun kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisan

Tinubu zai halarci jana'izar sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai halarci jana'izar sojojin da aka kashe a jihar Delta.

Shugaban ƙasan zai je wurin jana'izar ne wacce za a yi a maƙabartar ƙasa da ke Abuja, a matsayin babban baƙo na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel