Bashin da Ake Bin Najeriya Ya Karu, Ya Kai Naira Tiriliyan 97 a Mulkin Shugaba Tinubu
- A karshen shekarar 2023, adadin bashin da ake bin Najeria ya haura zuwa Naira tiriliyan 97.34, kusan karin kaso 10.73
- Rahoton hukumar kididdiga ta ƙasa (NBS) ya nuna cewa bashin ya karu ne idan aka kwatanta da bashin N87.91trn a zango na uku na 2023
- Haka zalika, rahoton hukumar ya nuna cewa jihar Legas da Delta sun karbi bashin waje da ya kai Naira tiriliyan 1.423
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Adadin bashin da ake bin Najeriya ya karu daga N87.91trn ($114.35bn) a zango na uku na shekarar 2023 zuwa N97.34trn ($108.23bn) a zango na hudu na shekarar 2023.
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana hakan a ranar Talata a cikin rahotonta na bashin cikin gida da na kasashen waje da ake bin Najeriya a zango na karshen 2023.
Bashin Najeriya ya karu da 10.73%
Rahoton kamar yadda jaridar The Nation ta gani, bashin da ake bin Najeriya wanda ya hada da bashin waje da na cikin gida ya karu da kashi 10.73.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya ce bashin waje ya kai Naira tiriliyan 38.22 ($42.50bn) a Q4-2023, yayin da bashin cikin gida ya kai Naira tiriliyan 59.12 ($65.73bn).
Duk da haka, bashin waje ya tsaya a kashi 39.26 a cikin Q4-2023, yayin da bashin cikin gida ya ke da kaso 60.74.
Bashin da ake bin jihohin Najeriya
Game da bashin da ake bin jihohi, jaridar Vanguard ta rahoto cewa jihar Legas ce ta fi yawan basussukan cikin gida da N1.05trn a cikin Q4-2023, sai Delta da ke biye da ita da N373.41bn.
Rahoton ya nuna jihar Jigawa ke da mafi karancin basussukan cikin gida da Naira biliyan 42.76, sai Kebbi da ake bi Naira biliyan 60.69.
Bugu da kari, rahoton ya bayyana cewa jihar Legas ce ta fi kowacce jiha yawan bashin waje da dala biliyan 1.24, sai jihar Kaduna da dala miliyan 587.07.
Borno ke da mafi karancin basussukan waje da dala miliyan 20.49, sai Yobe da dala miliyan 21.49.
Ana hasashen cewa akwai mutane kimanin miliyan 200 a Najeriya. Hakan yana nufin kowane ‘dan kasar nan yana da bashin kusan N520,000 a kansa a halin yanzu.
Bashin waje na Najeriya ya karu
Tun da farko, Legit Hausa ta ruwaito cewa bashin da kasashen Faransa, China, Indiya, Jamus da Japan ke bin Najeriya ya karu sosai.
Ofishin kula da basussukan Najeriya (DMO) ya bayyana cewa akalla kasashen biyar na bin Najeriya dala biliyan 5.
Asali: Legit.ng