Ministan Buhari Ya Ba Gwamnati Lakanin da Zai Yi Maganin ’Yan Bindiga a Ruwan Sanyi

Ministan Buhari Ya Ba Gwamnati Lakanin da Zai Yi Maganin ’Yan Bindiga a Ruwan Sanyi

  • Tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya ba gwamnatin tarayya shawarar yadda za ayi maganin 'yan bindiga a cikin sauki
  • Shittu, wanda tsohon minista ne a gwamnatin baya, ya ce akwai bukatar gwamnati ta yi zaman sulhu da 'yan bindiga
  • Ya ce idan aka saurari matsalolinsu kuma aka bunkasa rayuwarsu, zai kawo zaman lafiya, maimakon kashe kudi wajen sayen makamai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi zaman sulhu da 'yan bindiga a yunkurinta na magance matsalar tsaro a Najeriya.

Adebayo Shittu ya yi magana kan matsalar tsaro a Najeriya
Tsohon minista, Adebayo Shittu, ya fadi yadda gwamnati za ta yi maganin 'yan bindiga. Hoto: Adebayo Shittu
Asali: Twitter

Shittu, wanda tsohon minista ne a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Talata.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da matar Gwamnan PDP bayan musayar wuta? Gaskiya ta bayyana

"Gwamnati ba ta makaraba ba" - Shittu

Shittu ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Da ace ina da ƙarfin iko, da na yi zaman lalama da ƴan bindiga, na saurari matsalolinsu domin ba mu makara ba.
"Mu bunƙasa rayuwarsu, domin da yawansu na da kaifin basira, da yawansu na da sauran jini a jika."

A cewarsa, irin maƙudan kuɗaɗen da jami'an tsaro ke kashewa wajen mallakar makamai ya yi yawa, kuma ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Gwamnati ta yi sulhu da 'yan bindiga?

Tsohon ministan ya yi nuni da cewa miliyoyin yara da ke gararamba a titunan Najeriya ba tare da ilimi ba, su ne suke rikidewa zuwa ƴan ta'adda.

Shittu ya yi nuni da cewa akwai bukatar gwamnati ta yi zaman sulhu da ƴan bindiga tare da biya masu bukatunsu na rayuwa, musamman mayar da su matsugunansu.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnan PDP ya naɗa tsohon shugaban tsageru a matsayin Sarki mai martaba

Sai dai, jaridar Vanguard ta ruwaito Shittu na jaddada cewa abu mafi muhimmanci shi ne gwamnati ta samar da hanyoyin magance matsalar ƴan bindiga domin samar da zaman lafiya.

"Yan bindiga 'yan kasa ne" - Shittu

'Dan siyasar ya ce al'ummomi sun yi watsi da ƴan bindiga kamar yadda gwamnati taki sauraronsu, yana mai cewa su ma ƴan kasa ne kamar kowa.

Ya ce ma damar gwamnati ta yi zaman lalama da ƴan bindigar, ta ba su ilimi da bunƙasa rayuwarsu, to su ma za su ba da gudunmawa wajen ci gaban ƙasar.

"Maimakon mu ci gaba da kashe kudi wajen sayen makamai, zai fi mu samar da wata hanyar magance wannan matsalar ba tare da amfani da makami ba, mu yi zaman lalama da su."

A cewar Shittu.

Yan bindiga sun kai hari Katsina

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu gungun ƴan bindiga sun kai farmaki wani kauyen karamar hukumar Dutsinma, jihar Katsina ana shirin yin buda baki.

Rahotanni sun bayyana cewa a yayin farmakin, sun yi awon gaba da matan aure 12 tare da namiji daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.