Sulhu Da 'Yan Bindiga Ya Fi Kamata Tinubu Ya Yi, Ahmad Sani Yariman Bakura

Sulhu Da 'Yan Bindiga Ya Fi Kamata Tinubu Ya Yi, Ahmad Sani Yariman Bakura

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yariman Bakura, ya ce sulhu na gaskiya da 'yan bindiga zai taimaka wajen magance matsalar tsaro a Najeriya
  • Ya ce matsalar tsaron da ake fama da ita ba fin ƙarfin gwamnatin Najeriya ta yi ba, iyaka dai ba a bi hanyoyin da suka dace ba ne
  • Yarima ya kuma ce idan gwamnati ta yi sulhun ba tare da samun abinda ake so ba, sai ta yi amfani da ƙarfin soji wajen murƙushe duka 'yan ta'addan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yariman Bakura, ya ce yin sulhu da 'yan bindiga zai matuƙar taimakawa wajen shawo kan matsalar ta'addanci da ta addabi Arewacin Najeriya.

Yarima ya bayyana cewa yin sulhu irin wanda aka yi da tsagerun Neja Delta zai taimaka wajen magance matsalar tsaro da ta baibaye jihohin Arewa.

Kara karanta wannan

Pantami Ya Bayyana Kalubale 4 Da Ya Fuskanta Lokacin Da Ya Ke Ministan Buhari

Yarima ya bayyana hakan ne a wata hira da sashen Hausa na BBC a cikin shirinsu na gane mini hanya.

Sulhu a kamata gwamnati ta yi da 'yan bindiga
Sulhu na tsakani da Allah ya kamata gwamnati ta yi da 'yan bindiga. Hoto: Rabiu Lawal Bagaruwa Anka
Asali: Facebook

Yarima ya ce 'yan bindiga ba su fi ƙarfin gwamnati ba

Yarima ya ce matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya ba fin ƙarfin gwamnati ta yi ba. Ya ce muddun za a tashi tsaye, to lallai za a shawo ƙarshen matsalar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce lokacin da aka rantsar da shi gwamnan jihar Zamfara, ya tarar da matsalar 'yan fashi da makami, amma da ya ɗauki matakan da suka dace, an magance matsalar.

Wani ɓangare na jawabinsa na cewa:

“Don haka ina tabbata maka sojojin Najeriya suna da yawa, suna da bindigogi, suna da ƙarfin da za su iya kore waɗannan 'yan bindigan ɗin cikin ɗan lokaci kaɗan.”

Yarima ya nemi a yi sulhu da 'yan ta'adda irin wanda aka yi da 'yan Neja Delta

Kara karanta wannan

Sokoto: An Yi Jana'izar Mahaucin da Jama'a Suka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW, Shaidu Sun Bayyana Gaskiya

Ya ce tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙi ɗaukar mataki mai tsauri kan 'yan ta'addan ne, saboda ƙila bai son a zubar da jini da yawa.

Yarima ya shawarci gwamnatin Tinubu da ta fara gabatar da sulhu tsakaninta da 'yan bindigar kamar yadda aka yi wa 'yan Neja Delta.

Yarima ya ce idan hakan kuma bai yiwu ba, sai gwamnati ta yi amfani da ƙarfin soji wajen murƙushesu a duk inda suke.

Da aka tambayeshi kan ko menene dalilinsa na cewa a yi sulhu musamman in aka yi la'akari da cewa an yi sulhun a wasu jihohin can baya ba tare da samun abinda ake so ba, Yarima ya ce sulhun ba a yi shi na tsakani ga Allah ba.

Ya ce a duk sulhun da aka yi da 'yan ta'addan can baya, ba a cika musu alƙawuran da aka ɗauka ba.

Ya ce idan gwamnati ta zauna ta yi sulhu da su na gaskiya, ta sa ayi musu wa'azin da zai kore musu duhun jahilci, sannan a samar musu wani abun yi, to za a samu abinda ake so.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: Sabuwar Gwamnatin Zamfara Ta Yanke Hukunci Kan Yuwuwar Neman Sulhu da 'Yan Bindiga

Yarima ya bayyana cewa talauci da jahilci ne kan gaba wajen kawo matsaloli a cikin ƙasa, inda ya ce ya zama wajibi ga shugabannin su tashi su yi yaƙi tuƙuru da talauci da jahilci.

Yariman Bakura ya yabawa Tinubu bisa matakan da ya ɗauka

Yarima ya yabawa Shugaba Tinubu bisa ƙwararan matakan da ya ɗauka wajen cire tallafin man fetur, da kuma matakin da ya ɗauka kan canjin kuɗaɗen waje.

Ya ce Tinubu ya ɗauki ƙwarara matakan da da yawa daga shugabannin da suka shuɗe suka gagara ɗauka.

Ya bayyana cewa ko tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari sai dai ya sha alwashin aiwatar da hakan, amma bai yiwu ba har ya bar mulki.

Ya kuma yabawa shugaba Tinubu kan buɗe iyakokin Najeriya da aka yi domin ci gaba da shigowa da motoci domin haɓaka kasuwanci.

Bello Turji ya sako mutane 22 da yaransa suka yi garkuwa da su

Kara karanta wannan

Eid El Kabir: Portable Mai Wakar Zazu Ya Hargista Intanet Bayan Nuna Shanu 5 Da Raguna 2 Da Ya Siya Don Shagulgulan Sallah

A wani labarin na daban da Legit.ng ta kawo muku a baya kun karanta cewa, ƙasurgumin ɗan ta'addan nan Bello Turji, ya sako wasu mutane 22 da yaransa suka yi garkuwa da su.

Turji ya sako mutanen ne bayan shafe sama da kwanaki 50 a hannunsu, inda yaransa suka gana musu baƙar azaba a lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel