Rashin Tsaro: Abin Da Yasa Ƴan Najeriya Ba Za Su Iya Mallakar Makamai Ba, Ministan Ƴan Sanda

Rashin Tsaro: Abin Da Yasa Ƴan Najeriya Ba Za Su Iya Mallakar Makamai Ba, Ministan Ƴan Sanda

  • Muhammad Dingyadi, Ministan Harkokin Yan Sanda ya ce baya ra'ayi da kuma goyon bayan bawa yan Najeriya ikon mallakar makamai
  • Dingyadi ya ce kyalle yan Najeriya su rika mallakar makamai zai kara janyo tabarbarewar tsaro ne ba gyara ba
  • Ministan ya yi wannan jawabin ne yayin bada amsa ga Ado Doguwa, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisa da ya bada shawarar a kyalle yan Najeriya su kare kansu

FCT, Abuja - Ministan Harkokin Yan Sanda, Muhammad Dingyadi, ya ce matsalar tsaro a kasar zai kara tabarbarewa ne idan aka bari yan Najeriya suka mallaki makamai, Daily Trust ta rahoto.

Rashin Tsaro: Abin Da Yasa 'Yan Najeriya Ba Za Su Iya Mallakar Makamai Ba, Minista
Ministan Harkokin 'Yan Sanda, Muhammad Dingyadi. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne yayin wani hira da ya yi da manema labarai a ranar Alhamis a Abuja yayin amsa tambayoyi daga shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin tarayya, Ado Doguwa, wanda a makon da ya gabata ya ce a bari yan Najeriya su mallaki makamai don kare kansu duba da tabarbarewar tsaro a kasar.

Kara karanta wannan

Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya

Kyale 'yan Najeriya su mallaki makamai zai janyo karin matsalar tsaro, Dingyadi

Dingyadi ya ce:

"Muna iya kokarin mu domin ganin mun takaita wanzuwar bindigu a tsakanin yan Najeriya. Ya kamata mu takaita wadanda za su mallake su, wadanda za su yi amfani da su, wadanda za a horas su yi amfani da su da wadanda za su iya samunsu."
"Idan ba haka ba, idan ka bari kowa ya mallaki makamai, abin zai kara lalacewa. Wannan shine ra'ayi na. Bana goyon bayan hakan a yanzu," a cewar Ministan.

Leadership ta rahoto cewa ya kara da cewa ma'aikatarsa tana iya kokarinta domin tabbatar da karin albashi na jami'an yan sanda a dukkan sassan kasar.

'Yan Ta'adda Sun Afka Wa Mutane a Masallaci Yayin Buɗe-Baki, Sun Kashe 3 Sun Sace Wasu Da Dama

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Bidiyon busasshen tsohon da mutuwa ta mance dashi ya girgiza intanet

A wani labarin, A ranar Talata ‘yan bindiga sun kai farmaki masallaci inda suka afka wa wa mutane yayin da suke tsaka da yin buda-baki, wanda ya ja suka halaka mutane uku, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta gano yadda ‘yan ta’addan suka isa da yawansu, har suka sace wasu da yawa a masallacin sannan suka zarce da su inda ba a sani ba.

An tattaro bayanai akan yadda lamarin ya auku a kauyen Baba Juli da ke karamar hukumar Bali a cikin Jihar Taraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel