AYM Shafa: Attajiri Ya Ware Makudan Kudi Ga Iyalan Wadanda Suka Rasu Wajen Karbar Zakkah
- Yayin da ake cikin jimamin mutuwar wasu a yayin karbar zakka a Bauchi, AYM Shafa ya gwangwaje iyalansu da kyauta
- Kamfanonin ya ba iyalan wadanda suka mutu buhunnn shinkafa da masara da kuma N250,000 domin rage musu radadi
- Wannan na zuwa ne bayan wasu mata sun rasa rayukansu yayin cunkoson karbar Zakka a ranar Asabar da ta gabatar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - Kamfanin mai na AYM Shafa ya jajantawa iyalan wadanda suka rasu yayin ba da Zakka a Bauchi.
Kamfanin ya tura tawaga ta musamman domin yin jajen tare da ba su gudunmawa na kayan abinci.
Musabbabin ziyarar gidajen wadanda suka mutu
Tawagar ta kai ziyarar karkashin jagorancin malamin Musulunci, Dakta Ibrahim Disina, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Disina ya musu jaje a madadin kamfanin inda ya ce mai kamfanin, Alh Yakubu Maishanu ba ya Najeriya.
Ya bayyana cewa an ba da zakkar ta hannun Gidauniyar Abdulmumini a madadin AYM Shafa, cewar TheCable.
Yayin ziyarar jajen, kamfanin ya ba iyalan wadanda abin ya shafa kayan abinci da kuma makudan kudi.
Daga cikin kayan da aka ba su akwai buhunan shinkafa biyu da buhun masara da na gero da kudi N250,000 ga kowanensu.
Adadin mutanen da suka mutu ya karu
Alƙaluman mutanen da suka rasu a iftila'in da ya faru wurin rabon zakkah a jihar Bauchi ya karu zuwa mata bakwai.
Rundunar 'yan sanda reshen jihar Bauchi ita ta tabbatar da haka a ranar Litinin 25 ga watan Maris a Bauchi.
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, SP Ahmed Wakili ya tabbatar da hakan ga manema labarai inda ya wallafa sunayen wadanda suka mutu..
Mutane 7 sun mutu yayin karbar zakka
Kun ji cewa akalla mata bakwai ne suka mutu yayin cunkoson karbar Zakka a jihar Bauchi a karshen makon da ya gabata.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 23 ga watan Maris da ta gabata a kan hanyar Jos da ke jihar Bauchi.
Rundunar 'yan sanda a jihar ta tabbatar da mutuwarsu inda ta fitar da jerin sunayen matan da suka mutu.
Asali: Legit.ng