Kano: Abba Kabir Ya Tura Sunan Ɗan Kwankwaso da Mutum 3 Majalisa Domin Tantancewa

Kano: Abba Kabir Ya Tura Sunan Ɗan Kwankwaso da Mutum 3 Majalisa Domin Tantancewa

  • Yayin da ya shafe kusan watanni 10 kan mulki, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir ya tura sunayen mutane hudu Majalisar jihar
  • Gwamna ya tura sunayen nasu ne domin tantance su a matsayin karin kwamishinoni a jihar kan wadanda ake da su
  • Legit Hausa ta ji ta bakin hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren kafar sadarwa ta zamani kan wannan nadi da ake shirin yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sake tura sunayen mutane hudu Majalisar dokokin jihar domin tantance su.

Mai girma Abba Yusuf ya tura sunayen zuwa Majalisar ne domin tantance su a matsayin ƙarin kwamishinoni a jihar.

Kara karanta wannan

Bauchi: Adadin mutanen da suka mutu wajen rabon zakka ya harba, an samu jerin sunaye

Abba ya tura ɗan Kwankwaso da mutane 4 domin tantance su a Majalisar jihar Kano
Gwamnan Abba Kabir ya saka sunan ɗan Kwankwaso a jerin wadanda za a tantance a Majalisar jihar Kano. Hoto: @KwankwasoRM.
Asali: Twitter

Wasu sunaye Abba ya tura Majalisar Kano?

Daga cikin wadanda aka tura akwai ɗan tsohon gwamnan jihar, sanata Rabiu Musa Kwankwaso mai suna Mustapha Rabiu Kwankwaso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran wadanda ake so a nada cikin kwamishinoni sun hada da Adamu Aliyu Kibiya da Usman Shehu Aliyu da kuma Abduljabbar Garko.

Dalilin dakatar da kwamishina a Kano

Daga cikinsu akwai Adamu Aliyu Kibiya wanda shi ne aka dakatar kafin yanke hukuncin zaben jihar saboda katoɓarar da ya yi ga alkalan kotu.

Kibiya ya yi barazanar inda ya ke zargin akwai kullalliya cewa an ba alkakan kudi za su yi hukuncin da bai dace ba.

Daga bisani gwamnan jihar ya dakatar da shi bayan korafe-korafe daga jama'a wanda ake ganin barazana ce ga zaman lafiyar jihar.

A kwanakin baya, gwamnan ya ba kwamishinonin wa'adin kwanaki da su rubuto ayyukan da suka yi a ma'aikatunsu domin sanin makomarsu a gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya naɗa mutane sama da 250 a muhimman muƙamai ana tsaka da azumi

Mustafa Kwankwaso ya cancanta?

Legit Hausa ta ji ta bakin hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren kafar sadarwa ta zamani kan wannan nadi.

Salisu Yahaya Hotoro ya ce babu batun cece-kuce kan wannan saboda ɗan Kwankwaso shi ma ɗan kasa ne kuma ya na da gogewa da zai rike kowane mukami.

"Ɗan Kwankwaso shi ba ɗan jihar Kano ba ne? Shin akwai wata doka da ta ce shi ba zai rike wani mukami ba?
(Mustafa Kwankwaso) ya yi karatu ya na da gogewa na rike dukkan mukamin da aka ba shi."
"Bayan haka ba yau ya shiga siyasa ba duk kamfe da shi muka yi a kananan hukumomi 44, ya ba da dukkan gudunmawa."

- Salisu Yahaya Hotoro

Hotoro ya ce shi bai ga abin cece-kuce kan wannan lamari ba, ko da kuwa Rabiu Kwankwaso ne ya tura sunansa ai hidimar da ya yi wa jihar Kano da NNPP ya cancanci a ba shi kowace irin kujera.

Kara karanta wannan

Gumi ya taka rawa wurin kubutar da dalibai 137 a Kaduna? Uba Sani ya fayyace gaskiya

Abba Kabir ya tausayawa wasu ƙauyuka

A baya, mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kai ɗauki ga wasu ƙauyukan jihar kan rashin ruwan sha.

Ƙauyukan sun hada da Danya da Kyallin Bula wadanda suka dade cikin halin matsin rashin ruwan sha a ƙaramar hukumar Bichi.

Ƙauyukan sun shafe shekaru a wahala sakamakon wuyar da suke sha wajen samun ruwan da za su yi amfani da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel