Kamfanoni 15 da za su rinka shigo da man fetur Najeriya a bana
A wani yunkurin na wadatar da kasar nan da man fetur, shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, Mele Kolo Kyari, ya ce kamfanin na shirin hada gwiwa da wasu 'yan kasuwanni masu zaman kansu domin tabbatar da ci gaban kasa.
Kamfanin man fetur na Najeriya a ranar Lahadi, 18 ga watan Agustan 2019, ya fidda sunayen kamfanoni 15 da aka bai wa kwantaragin tace danyan man fetur wanda zai wadatar da kasar a bana.
Kyari wanda ke kokarin kara tabbatar da gaskiya a al'amuran kamfanin, ya shaidawa manema labarai na jaridar Premium Times wannan sabuwar wallafa ta sunayen kamfanonin da za su shige gaba wajen gudanar da harkokin man fetur a kasar.
Makonnin kadan da suka gabata, Kyari wanda aka nada jagorancin kamfanin man fetur a watan Yuli, ya ce zai wallafa sunayen wadanda za su gudanar da kwangilar danyen man fetur ta kasar da kuma kamfanonin da suka taki nasarar samun aikin musayar danyan mai na Najeriya da tace shi.
Ga jerin sunayen kamfanonin 15 kamar yadda kakakin kamfanin, Ndu Ughamadu ya bayyana:
1. BP OIL INTERNATIONAL LTD./AYM SHAFA LTD.
2. VITOL SA/CALSON-HYSON
3. TOTSA TOTAL OIL TRADING SA/TOTAL NIG. PLC
4. GUNVOR INTERNATIONAL B.V./AY MAIKIFI OIL & GAS CO. LTD.
5. TRAFIGURA PTE LTD./A. A. RANO NIG. LTD
6. CEPSA S.A.U./OANDO PLC
7. MOCOH SA/MOCOH NIG. LTD.
8. LITASCO SA/BRITTANIA-U NIG. LTD./FREEPOINT COMMODITIES
9. MRS OIL & GAS COMPANY LTD
10. SAHARA ENERGY RESOURCE LTD
11. BONO ENERGY LTD./ETERNA PLC/ARKLEEN OIL & GAS LTD./AMAZON ENERGY
12. MATRIX ENERGY LTD./PETRATLANTIC ENERGY LTD./UTM OFFSHORE LTD./LEVENE ENERGY DEVELOPMENT LTD
13. MERCURIA ENERGY TRADING SA/ BARBEDOS OIL & GAS SERVICES LTD./RAINOIL LTD./PETROGAS ENERGY
14. ASIAN OIL & GAS PTE LTD./ EYRIE ENERGY LTD./ MASTERS ENERGY OIL & GAS LTD/CASIVA LTD
15. DUKE OIL COMPANY INCORPORATED.
KARANTA KUMA: Gwamna Matawalle ya nada sabon shugaban ma'aikatan jihar Zamfara
Sabon shugaban kamfanin ya ce bayyana ayyukan kamfanin da kuma shirin bunkasa harkar cinikayyar man fetur na kasar zai bunkasa zuba jari, wanda a baya a ya durkushe saboda rashin gaskiya.
Jaridar BBC Hausa ta ruwaito cewa, an dai kwashe shekaru ba a wallafa bayanan irin wadanda kwangiloli ba, kuma a cikin shekaru da dama ana yi wa kamfanin kallon wanda ke cike da ayyukan rashawa, lamarin da ya sha musantawa.
Kyari ya ce akwai bukatar farfado da matatun man fetur na gwamnati,wanda ya ce muddin hakan ya tabbata Najeriya za ta iya zamowa mai samar da mai ga nahiyyar Afirka baki daya.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng