Bauchi: Adadin Mutanen da Suka Rasu a Wurin Rabon Zakkah Ya Ƙaru, An Faɗi Sunayensu

Bauchi: Adadin Mutanen da Suka Rasu a Wurin Rabon Zakkah Ya Ƙaru, An Faɗi Sunayensu

  • Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa adadin matan da suka rasu sakamakon turmutsutsi a wurin rabon zakkah a Bauchi ya ƙaru
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili, ya ce mata 6 sun rasu a asibitin koyarwa yayin da ɗaya ta ƙarisa a gida
  • Lamarin dai ya faru ne yayin da mutane suka taru a kamfanin Shafa Holdings da ke kusa da titin zuwa Jos a garin Bauchi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Alƙaluman mutanen da suka rasu a ibtila'in da ya faru wurin rabon zakkah a jihar Bauchi a ƙarshen maƙon nan ya karu zuwa mata bakwai.

Rundunar ƴan sanda reshen jihar Bauchi ce ta tabbatar da haka ranar Litinin, 25 ga watan Maris, 2024, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsadar iskar gas: Jigon APC ya bukaci Shugaba Tinubu ya tausayawa talaka

Sufetan yan sanda na kasa, IGP Kayode.
Yan sanda sun ce mata 7 ne suka mutu a wurin rabon Zakkah a Bauchi Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

An tabbatar da mutuwar mutum shida daga ciki a asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi yayin da ragowar ɗaya ta ƙarisa a gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka yayin da yake ƙarin haske kan turmutsitsin da aka yi a wurin rabon zakkah.

Waɗanda suka mutu duk mata ne

Kakakin ƴan sandan ya ambaci sunayen waɗanda suka mutu, ga su kamar haka:

1. Aisha Usman, ƴar kimanin shekara 13 daga yankin Gwang Gwang Gwang a Bauchi.

2. Sahura Abubakar ƴar kimanin shekara 55 a duniya

3. Aisha Abubakar ƴar kimanin shekara 45 da ke zaune a layin Kabo cikin jihar Bauchi

4. Khadijah Isah ƴar kimanin shekara 8 a duniya daga yankin Karofi a Bauchi

5. Maryam Suleiman ƴar shekara 20 daga yankin Kandahar

Kara karanta wannan

Filato: An shiga tashin hankali bayan sabon rikici ya barke, bayanai sun fito

6. Maryam Shuaibu ƴar shekara 16 daga yankin Gwang Gwang Gwang.

7. Hassana Saidu yar ƙimanin shekara 53 daga Dutsen Tanshi a Bauchi.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a kamfanin Shafa Holdings Plc daura da hanyar Jos a cikin babban birnin Bauchi.

Mazauna garin da dama sun taru a kamfanin don karbar N10,000 kowanne a matsayin zakkah ga talakawa wanda wani attajiri ya fitar.

Sai dai an samu hargitsi a yayin taron, wanda ya haifar da turmutsutsin da ya yi ajalin mata har mutum bakwai, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

An biya kuɗin fansar ceto ɗaliban Kuriga?

A wani rahoton kuma Malam Uba Sani ya bayyana cewa ko kaɗan cece-kuce kan batun biyan kuɗin fansa wajen ceto ɗaliban Kuriga ko akasin haka ba shi da amfani.

Gwamnan ya ce mafi muhimmanci shi ne daliban sun dawo gida cikin ƙoshin lafiya kuma gwamnati ta yi iya bakin ƙoƙarinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel