Kurkunkus: Kotu ta Baiwa DSS Umarni 1 Kan Tukur Mamu da Ake Zargi da Sasanci da 'Yan Ta'adda

Kurkunkus: Kotu ta Baiwa DSS Umarni 1 Kan Tukur Mamu da Ake Zargi da Sasanci da 'Yan Ta'adda

  • Wata kotu da ke zama a Kaduna ta umarci jami'an tsaro na farin kaya da su gaggauta mika Tukur Mamu gaban kotu idan sun kama shi da laifi
  • Mamu ta hannun lauyoyinsa ya bukaci kotun ta bai wa DSS umarnin basi hakkinsa na 'dan Adam wanda kuma ta amsa bukatar
  • Tun a watan Satumban 2022 DSS ta tsare Mamu bayan dawo da shi daga Cairo kan zargin hadin baki da 'yan ta'adda wurin karbar kudin fansa

Kaduna - Wata babbar kotun jihar Kaduna ta umarni hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS da ta hanzarta mika Tukur Mamu zuwa kotu idan an kama shi da wani laifi kan zargin hannunsu wurin cinikayyar kudin fansa a madadin 'yan ta'addan da suka sace fasnjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wani Mai Hannu a Harin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja, An Gano Abu 3

Malam Tukur Mamu
Kurkunkus: Kotu ta Baiwa DSS Umarni 1 Kan Tukur Mamu da Ake Zargi da Sasanci da 'Yan Ta'adda. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Mamu, mawallafin jaridar Desert Herald kuma mai magana da yawun Sheikh Ahmad Gumi, fitaccen malamain addinin Islama mazaunin Kaduna, an kama shi a birni Alkahira da ke kasar Masar a ranar 6 ga watan Satumban 2023 yayin da ya ke hanyarsa ta zuwa kasa mai tsarki tare da iyalansa.

Mamu, wanda ya ke kan gaba wurin sasanci domin sako fasinjojin jirgin kasan Kaduna, an tsare shi a filin jirgin sama na Al-Kahira inda daga bisani aka dawo da shi Najeriya tare da damka shi a hannun jami'an DSS. Tun daga nan yake a tsare.

A wata bukata da ya shigar gaban kotu a ranar 22 ga watan Nuwamban 2022 ta hannun lauyoyinsa, Muhammad Sani Katu, SAN, Solomon Utuagha Esq, Auwal Muktar Sirajo Esq da Aisha Musa Esq sun bukaci:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Umarnin da a tirsasa bai wa wanda ke kara hakkinsa na 'dan Adam da ke kunshe kuma ake bashi kariya a sassa na 34,35,36 da 41 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yankewa Matashi Hukuncin Kisa Kan Satar N57,000 a Jihar Legas

Umarnin da a tirsasa bai wa wanda ke kara hakkinsa na 'dan Adam da ke kunshe kuma ake bashi kariya a sassa na 34,35,36 da 41 n2a kundin tsarin mulkin Najeriya na 199.

Umarni na biyu na hakkokin 'dan Adam na 2009 da takardu na 3,5 da 6 na African Charter da hakkin jama'a wanda ake takewa ko za a iya takewa daga wadanda ake kara, jami'ansu ko wakilansu.

A zaman kotun da aka yi a ranar Litinin, alkalin kotun Jastis Edward Andow, ya amsa bukata daya ta wanda ke karar na a aike shi gaban kotu idan bukatar hakan ta taso.

Yayin amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan zaman kotun, shugaban lauyoyin Mamu, Muhammad Sani Katu, yace ya gamsu da umarnin kotun kuma ya bayyana cewa yana da yakinin DSS zasu aikata.

DSS sun shiga gidan Mamu, sun kwashe kwamfuyutoci da takardu

A wani labari na daban, jami'an hukumar tsaro na farin kaya, DSS, sun shiga gidan Tukur Mamu, hadimin Sheikh Gumi da ake zargi da alaka da 'yan bindiga.

Sun yi bincike a gidan inda suka kwashe wasu takardu tare da kwamfuyotoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel