Hanyoyi 5 da arewa zatabi domin magance talauci a yankin - Senata Shehu Sani
- Senata Shehu sani yayi na'am da cewa akwai matsalar talauci a arewacun Najeriya
- Senatan yayi kira ga shugabanin arewa su maida hankali wajen nemo hanyoyin rage talauci a yankin
- Daga cikin shawarwarin da ya bada, Sani yac dole 'yan arewa su rage dogaro akan man fetur
Senata Shehu Sani ya amince da cewa dimbin mutanen yankin arewa na fama da talauci amma yace shugabanin yankin ne ke iya tsamo arewar daga cikin wannan halin da ta tsinci kanta.
A wata hira da yayi da jaridar Daily Independent, yace: ''Zanyi amfani da wannan damar domin in tunatar da jama'a musamman 'yan arewa, da cewa akwai hanyoyin da zamu iya bi domin tattalin arzikin mu ya bunkasa kamar na wasu yankuna da ke samar da ma'adinan da Najeriya ke dogara dashi.''
Hanyoyin da ya lisafo kuwa sune:
1. Dole ni mu nisantar da kanmu daga ayyukan ta'adanci da kuma mutane masu tsatsauran ra'ayi, wannan yana da muhimmanci sosai.
2. Dole ne mu rage dogaro akan man fetur.
3. Mu kara maida hankali da kuma saka jari a fanin ilimi, domin ilimi ne ke ciyar da sauran sasan rayuwa gaba.
4. Dole ne mu saka jari sosai a cikin harkan noma da masana'antu.
DUBA WANNAN: Hukumar NNPC zata horar da ma'ikatan ta dabarun yaki cin hanci da rashawa
5. Akwai bukatan hadin kai, zaman lafiya da girmama juna tsakanin mabiya addinan musulunci da kirista a yankin. Duk wanda ke zaune a kowane gari ko jiha a yankin yana da daraja da mutunci a matsayinsa na dan adam.
A kwanakin baya Legit.ng ta kawo muku rahoto inda jagoran gwamnonin arewa Alhaji Kashim Shettima yake bayyanawa cewa yankin arewa ya zama abin dariya domin yadda talauci da rashin tsaro yayi wa yankin katutu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng