Mambila: An Tona Yadda Aka Nemi Amfani da Kaidin Mata a Yaudari Wasu Ministoci
- Gwamnatin Najeriya ta bankado yadda jami'in kamfanin Sunrise, Leno Adesanya, yake amfani da kaidin mata wajen neman kwangiloli
- Wannan na daga cikin hujjoji da gwamnatin ta gabatar gaban babbar kotun tarayya, a shari'ar da ƙasar ke yi da Sunrise kan kwangilar Mambila
- Gwamnatin na zargin Adesanya, jami'in Sunrise da ƙulla gadar zare wa tsofaffin ministocin Buhari domin samun kwangilar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gwamnatin Najeriya ta yi bayani kan tuhumar cin hanci da rashawa da take yi wa Leno Adesanya, jami'in kamfanin Sunrise and Transmission.
Gwamnati ta yi wannan bayanin ne a cikin takardun da ta gabatar wa babbar kotun tarayya da ke Abuja, kamar yadda jaridar The Cable ta gani.
A cikin takardun ƙarar da ta shigar, Olu Agunloye, tsohon ministan makamashi, ya gabatar da takardu wadanda gwamnati ta yi amfani da su wajen kafa hujja kan zarge-zargenta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin Adesanya ya yi karar gwamnati
Gwamnati ta yi zargin cewa Adesanya ya yi amfani da mata da kudi a matsayin cin hanci ga wasu ministocin gwamnatin Muhammadu Buhari domin ya samu kwangilar wutar Mambila.
Kamfanin Sunrise ya shigar da Najeriya kara a kotun ƙasa da ƙasa ta ICC da ke Paris, birnin Faransa, inda ya ke neman diyyar $2.3bn.
Kamfanin na neman diyyar ne saboda gazawar gwamnatin Najeriya na ba shi aikin wutar Mambila kamar yadda suka cimma yarjejeniya da Agunloye kafin a sauke shi daga mukaminsa.
Yadda Adesanya ke ba da cin hanci
A takardun hujjoji da Agunloye ya gabatarwa kotu a ranar 26 ga watan Fabrairu, 2024, ya nuna cewa Adesanya na amfani da mata da kudi wajen yaudarar ministoci.
Bayanan sun nuna cewa:
"A ranar 9 ga watan Nuwamba, 2019, Adesanya ya yi kokarin ba tsohon ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu cin hanci ta hanyar amfani da kudi da mata.
"Haka zalika ya so yin amfani da mata da kudi wajen toshe bakin tsohon Alkalin Alkalai na ƙasa, Abubakar Malami, domin goya wa kamfanin Sunrise baya wajen samun kwangilar."
Wasu hotuna da aka gabatar matsayin hujja sun nuna hotunan matan da Adesanya ya tura wa Adamu da Malami a lokuta daban daban a shafin WhatsApp.
Kalli hotunan a kasa:
Kwangilar Mabila: Buhari, Obasanjo sun magantu
Gwamnatin Najeriya ta shaida wa kotun cewa Adesanya na amfani da 'lagon' ma'aikatan gwamnati wajen ba su cin hanci domin kamfaninsa ya samu kwangila a ƙasar.
Idan ba a manta ba, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fito ya ce zai bayar da shaida kan badaƙalar kwangilar wutar Mambila.
Haka zalika, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nesanta kansa daga zargin sa da hannu a yarjejeniyar $200m da Najeriya ta cimmmawa da kamfanin Sunrise a 2020.
Badaƙalar Mambila: An kulle ministan Obasanjo
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta garkame Olu Agunloye, tsohon ministan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Agunloye bisa zarginsa da hannu a karkatar da $6bn na kwangilar wutar lantarki ta Mambila.
Asali: Legit.ng