Buhari Yayi Maganar Badakalar Mambilla da EFCC Ta Fara Binciken Manyan Gwamnati

Buhari Yayi Maganar Badakalar Mambilla da EFCC Ta Fara Binciken Manyan Gwamnati

  • Muhammadu Buhari ya aika wasika zuwa ga babban lauyan gwamnati domin wanke kan shi daga badakalar kwangilar Mambilla
  • Wasu jami’an gwamnati sun kulla yarjejeniya da kamfanin Sunrise Power, aka shirya za a biya su $200m idan sun janye kara a kotu
  • A bayaninsa, Muhammadu Buhari ya ce da yake kan kujerar mulki bai amince a biya wadannan kudi ba domin bai ga wani dalili ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Katsina - Muhammadu Buhari ya ce bai taba amincewa a biya wasu kudi domin a sasanta da kamfanin lantarki na Sunrise Power ba.

A wata wasika, The Cable ta ce tsohon shugaban Najeriyan ya wanke kan shi daga zargin biyan wasu kudi a kan kwangilar Mambilla.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Gwamnati za ta fara raba kyautan kudi ga talakawa miliyan 12, Minista

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari ya gaza karasa aikin Mambilla Hoto: Getty Images/www.power-technology.com
Asali: Getty Images

Tarihin Sunrise Power da aikin Mambilla

Kafin nan, Olusegun Obasanjo ya yi irin wannan zance, ya nuna bai amincewa Olu Agunloye shiga yarjejeniyar $6bn da kamfanin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A shekarar 2017, kamfanin wutan na Sunrise Power ya kai karar gwamnatin Najeriya a kotun duniya (ICC) bisa zargin sabawa alkawari.

Mambilla: Gwamnatin Buhari ta shigo zancen

Ana haka ne sai Abubakar Malami SAN a lokacin yana ministan shari’a, ya yarda gwamnati ta biya $200m domin a hakura da karar.

Amma kuma Muhammadu Buhari bai biya wadannan kudi kamar yadda AGF dinsa ya so ba, haka wa’adin ya wuce ba a biya ko sisin ba.

Buhari bai yarda a biya Sunrise Power $200m ba

A wata wasika da Nairaland ta ce Muhammadu Buhari ya aikawa Lateef Fagbemi, ya dage cewa bai yi na’am da biyan wadannan $200m ba.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta gama shirin raba buhuna miliyan 1.4 na kayan abinci a jihohi - Minista

Tsohon shugaban ya sanar da sabon ministan shari’ar ba da hannunsa aka yi maganar a sasanta da Sunrise Power a wajen kotu ba.

Me wasikar Muhammadu Buhari ta kunsa?

"Duk da na fahimci kamfanin Sunrise ya tuntubi ministocin shari’a, makamashi da na harkokin ruwa kuma an tattauna da masu ruwa da tsaki a harkar kwangilar,"
"Babu lokacin da na ba su umarni na musamman cewa su sasanta da kamfanin Sunrise Power and Transmission Company Limited."
"Shakka babu, a lokacin da aka kawo mani shawarar sa hannu a biya kudin sasantawa ranar 20 ga Afrilu 2020, na ki yarda a biya,"
"domin na gamsu babu dalilin da Sunrise za su nemi wadannan kudi."

- Muhammadu Buhari

Ministan Buhari ya shiga uku?

A shari’ar da aka yi, an ji yadda Najeriya ta nesanta kan ta daga yarjejeniyar da aka shiga. A kan wannan aka jefa Abubakar Malami a matsala.

Sunrise Power Ltd ya ce an soke yarjejeniyar aikin wutan lantarkin Mambilla da aka yi da shi a shekarun baya, gwamnati ta musanya batun nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel