An Samu Asarar Rayuka Bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Jami'an 'Yan Sanda

An Samu Asarar Rayuka Bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Jami'an 'Yan Sanda

  • Wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar ESN/IPOB ne sun kashe jami’an ƴan sanda biyu a wani sabon hari da suka kai wa jami’an tsaro a jihar Imo
  • Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Henry Okoye, ya ce ƴan bindigan sun yi wa jami’an dirar mikiya ne a lokacin da suke aikin sintiri
  • Okoye ya ce yayin da ƴan sanda biyu suka rasa rayukansu wasu guda huɗu sun tsira da rayukansu a safiyar Asabar, 23 ga watan Maris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Owerri, jihar Imo - Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton ƴan ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biyafara (IPOB) ne, sun harbe jami’an ƴan sanda biyu har lahira a jihar Imo.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile yunkurin yin garkuwa da mutane a Kaduna

Ƴan bindigan sun yi wa jami’an ƴan sandan dirar mikiya ne a lokacin da suke sintiri a tsohuwar hanyar Gariki, a ƙaramar hukumar Okigwe a jihar Imo a ranar Asabar, 23 ga watan Maris 2024.

'Yan sanda sun halaka jami'an tsaro
'Yan sanda sun halaka 'yan sanda biyu a jihar Imo Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Henry Okoye, wanda ya bayyana hakan, ya ce biyu daga cikin ƴan sandan sun rasa rayukansu, yayin da wasu guda huɗu suka tsira daga harin bayan musayar wuta da maharan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"An yi wa jami’an kwanton ɓauna ne da sanyin safiyar yau Asabar, 23 ga watan Maris 2024 a lokacin da suke aikin sintiri a tsohuwar hanyar Gariki Okigwe inda wasu miyagu suka jefi motarsu da wani abun fashewa.
"A sakamakon hakan, biyu daga cikin jami'an sun rasa rayukansa yayin da wasu guda huɗu suka tsira daga harin.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An bayyana abin da El-Rufa'i da Peter Obi za su yi wa Tinubu

Okoye ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Aboki Danjuma ya yi kira da a tsaurara matakan tsaro domin hana afkuwar lamarin nan gaba.

Ya ce jami’an ƴan sandan biyu suna aiki da Mopol 18, kamar yadda gidan talabijin na Channels tv ya ruwaito.

Ƴan sanda sun daƙile hari

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an ƴan sanda sun daƙile wani yunƙurin ƴan bindiga na sace mutane a jihar Kaduna.

Jami'an ƴan sandan sun yi musayar wuta da ƴan bindigan inda suka raunata da dama daga cikinsu a kan hanyar Buruku zuwa Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel