'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Katsina, Sun Hallaka Babban Dan Siyasa da Sace Iyalansa

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Katsina, Sun Hallaka Babban Dan Siyasa da Sace Iyalansa

  • An shiga jimami a jihar Katsina bayan ƴan bindiga sun kai harin ta'addanci a ƙauyen Mairuwa na ƙaramar hukumar Faskari
  • A yayin harin sun hallaka mutum biyu ciki har da wani babban ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa a ƙauyen
  • Miyagun sun kuma yi awon gaba da mata da ƴaƴa mata biyu na ɗan siyasan da aka bayyana sunansa a matsayin Alhaji Lado

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Mairuwa da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Miyagun ƴan bindigan sun kai harin ne a daren ranar Asabar, 23 ga watan Maris, 2024 inda suka kashe masallata.

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
'Yan bindiga sun kai sabon hari a Katsina Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Aƙalla mutane biyu ne aka harbe har lahira yayin da wani kuma ya samu rauni yayin harin.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Atiku ya caccaki Tinubu, ya fadi hanyar kawo karshen matsalar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ɗaya daga cikin waɗanda suka rasa ransu wani fitaccen mutum ne mai suna Alhaji Lado.

Yadda lamarin ya auku

Ana zargin cewa dai maharan sun kawo harin ne musamman saboda shi.

Wata majiya da ta bayyana marigayin a matsayin ɗan kasuwa, ɗan siyasa kuma babban manomi, ta ce marigayin an kashe shi ne lokacin da ya ƙi yarda ya bi ƴan bindigan.

A kalamansa:

"Sun buɗe masa wuta lokacin da suka yi yunƙurin sace shi amma ya ƙi bin su.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira daga harin a masallacin ya bayyana cewa maharan sun yi garkuwa da mata da ƴaƴa mata guda biyu na Alhaji Lado.

Wani ganau ya bayyana cewa, ɗayan mutumin da aka kashe a harin, ma’aikacin lafiya ne mai suna Sani.

A cewarsa:

"Yana aiki ne a asibitin Mairuwa."

Kara karanta wannan

'Ƴan bindiga sun kashe basarake da wasu mutum 20, sun tafka mummunar ɓarna a watan azumi

Me ya kawo ƴan bindiga ƙauyen?

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin garin Funtua, mai suna Abdulrahman Nasir, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun zo ne da niyyar sace Alhaji Lado amma sai ya ƙi binsu wanda hakan ya sanya suka harbe shi har lahira.

Ya yi bayanin cewa yana tunanin ƴan bindigan sun zo ne daga yankin Sheme, wanda yake kusa da ƙauyen na Mairuwa.

Ƴan bindiga sun hallaka ƴan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyaguj ƴan bindiga sun hallaka jami'an ƴan sanda biyu a wani hari a jihar Imo.

Ƴan bindigan sun hallaka jami'an tsaron ne bayan sun jefa musu wani abun fasshewa yayin da suke gudanar da aikin sintiri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel