Abin da Bola Tinubu Ya Faɗawa Sanatoci a Wurin Buɗa Bakin Azumin Watan Ramadan a Villa
- Bola Ahmed Tinubu ya lashi takobin cewa gwamnatinsa ba za ta zura ido ta yi shiru ba kan kisan dakarun sojoji a jihar Delta
- Yayin da ya karɓi bakuncin sanatoci a wurin buɗa baki, Tinubu ya ce waɗanda suka kashe sojoji a Okuama za su ɗanɗana kuɗarsu
- Shugaban ƙasar ya jaddada cewa rundunar sojin Najeriya na iya bakin kokarinta a yaƙi da matsalar tsaro kuma gwamnatinsa za ta ci gaba da mara masu baya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin cewa makasan sojoji Najeriya a jihar Delta ba za su ci bulus, su tafi haka kawai ba tare da an hukunta su ba.
Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci hare-haren da ake kai wa dakarun sojoji da sauran jami'an tsaro ba.
Shugaban ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi bakuncin shugabannin majalisar dattawa a wurin buɗa bakin azumin Ramadan a fadar shugaban kasa ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya karƙashin jagorancinsa za ta ci gaba da bai wa sojoji dukkan goyon bayan da suke buƙata domin murƙushe kowane irin ƙalubalen tsaro.
Abin da Tinubu ya faɗawa sanatoci
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajure Ngelale ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Alhamis, 21 ga watan Maris, 2024.
A sanarwar da babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin hulɗa da jama'a, Fedrick Nwabufo, ya wallafa a manhajar X, Tinubu ya gode wa majalisar dattawa bisa haɗin kan da suka ba shi.
Bola Tinubu ya ce:
"Dakarun sojojinmu suna aiki tuƙuru, kuma ba za mu ƙyale masu kai hare-hare su lalata mutunci da kimar rundunar sojojinmu da jagororinsu ba.
"Ba za muyi ƙasa a guiwa ba zamu ci gaba da yaƙi domin tabbatar da ƴancin mu na zama lafiya, kuma zamu yi nasara a koƙarin kawar da talauci daga kasarmu."
ƴan sandan jihohi: Ina aka kwana?
A wani rahoton kuma gwamnoni 16 ne suka ayyana goyon bayan kafa rundunar ƴan sandan jihohi yayin da matsalar tsaro ke kara karuwa a Najeriya.
Majalisar tattalin arzikin ƙasa ta tabbatar da haka ga manema labarai a Abuja ranar Alhamis, 21 ga watan Maris bayan kammala taro.
Asali: Legit.ng