Kisan Sojoji a Delta: Daga Karshe An Fadi Dalilin da Ya Sa Aka Kashe Jami'an Tsaron

Kisan Sojoji a Delta: Daga Karshe An Fadi Dalilin da Ya Sa Aka Kashe Jami'an Tsaron

  • Wani mazaunin ƙauyen Okuama da ke jihar Delta ya yi zargin cewa sojoji 16 da aka kashe a cikin garin ba su zo domin wanzar da zaman lafiya ba
  • Matashin ya yi iƙirarin cewa sojojin da suka rasa ransu, suna kan aikin kare muradun Tompolo ne
  • Kisan sojojin wanda ya faru a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, ya girgiza yankin Kudu maso Kudu da ƙasa baki ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Okuama, jihar Delta - Wani matashi ya fitar da wani faifan bidiyo yana mai iƙirarin cewa yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kashe sojoji 16 a jihar Delta.

Matashin wanda bai ambaci sunansa a cikin faifan bidiyon ba, ya ce ƙauyukan biyu suna rigima kan filaye ne wacce ta haifar da rikici.

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina ya fadi abin da ya kamata al'ummar jihar su yi domin kawo karshen 'yan bindiga

An fadi dalilin kashe sojoji a Delta
Matashi ya fito ya fadi dalilin kashe sojoji a Delta Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Sai dai, matashin ya zargi gwamnati da shugabanni da rashin kiran al’ummomin biyu domin a sasanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka kashe sojojin?

A cewarsa, jami’an tsaron da aka kashe da suka zo Okuama, masu biyayya ne ga Government Oweizide Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo.

A kalamansa:

"Wannan shi ne bidiyo na ƙarshe da zan yi kan faɗa tsakanin al’ummar Okuama da Okoloba.
"Ƴan ƙabilar Ijaw daga ƙauyen Okuama sun yi amfani da sojoji wajen ɗaukar mutane uku daga Okoloba suka kashe su. Mutanen uku duk an kashe su.
"Gwamnatin tarayya ta bai wa wasu mutane ikon satar man fetur kuma bayan sun yi satar, sojoji suna yi musu jagora domin sayar da man. Sun ci amanar ƴan’uwansu da jininsu."

Sojoji na da hannu a rikicin ƙauyukan

Bugu da ƙari, matashin ya yi zargin cewa mutumin da ke kula da satar man fetur ɗin ya yi amfani da sojoji wajen ɗauke mutane uku daga cikin ƙauyensu kafin ya kashe su.

Kara karanta wannan

Ramadan: Magidanci ya bayyana yadda yake tafiya mai nisa don samun abincin buda baki ga iyalansa

A kalamansa:

"Sojoji 16 an kashe su ne a lokacin da suka zo ɗaukar shugabannin ƙauyenmu, kuma matasan sun san cewa idan suka tafi da su (shugabannin) sai yadda aka yi sa su. Hakan ne ya sa aka kaiwa sojoji 17 hari.

Ya ƙara da cewa:

"Mahaifina jami’in soja ne mai ritaya wanda ya rasu a shekarar da ta. Na rasa mutane shida a fada tsakanin ƙauyukan Okuama da Okoloba.
Gwamnatin tarayya za ta iya bayyana ana nema na ruwa ajallo bayan yin wannan bidiyon."

Majalisa ta gana da hafsoshin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanatoci da hafsoshin tsaro a Najeriya sun shiga ganawar sirri kan kisan sojoji 16 a jihar Delta.

Hafsoshin tsaron sun gurfanar ne a gaban kwamitocin sojojin ruwa da na sama da kuma na kasa kan fara bincike game da lamarin a jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel