Daukar Nauyin Ta'addanci: Sheikh Gumi Ya Fadi Yadda Miyagun Ke Samun Kuɗi

Daukar Nauyin Ta'addanci: Sheikh Gumi Ya Fadi Yadda Miyagun Ke Samun Kuɗi

  • Yayin da ya ke kiran sulhu da 'yan bindiga, Sheikh Ahmed Gumi ya yi fatali da zargin da ake yi wasu na daukar nauyin 'yan ta'addan
  • Sheikh Gumi ya ce shiririta ne daurawa wasu tsiraru laifin daukar nauyin ta'addanci a Najeriya a halin yanzu
  • Ya ce maharan da kansu suke samun kuɗi wurin yin amfani da kudin fansa na biliyoyi da suke karba a hannun mutane

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi ya yi fatali da rahoton cewa wasu na daukar nauyin ta'addanci.

Gumi ya ce 'yan ta'addan ba su bukatar tallafin kudi daga hannun wasu tsiraru inda ya ce kudin fansa da suke karba ya ishe su, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Daukar nauyin ta'addanci: Sheikh Gumi ya fadi abin da ya dace a yi wa Tukur Mamu

Gumi ya yi fatali da zargin

Wannan na zuwa ne bayan gwamnati ta fitar da sunayen mutane da masu hada-hadar daloli da ake zargin su na daukar nauyin ta'addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin yayin tattaunawa da jaridar ya ce kotu ce kadai ta ke da ikon ayyana wani a matsayin mai daukar nauyin ta'addanci.

"Ina tunanin lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta dauki mataki kan matsalar 'yan bindiga domin dakile ta."

- Sheikh Gumi

Gumi: Yadda mahara ke samun kuɗi

"Yanzu su na neman biliyan ɗaya bayan sace daliban makaranta, wannan shi ne hanyar da suke samun kuɗi."
"Wannan shirme ne a ce wai wasu na daukar nauyin ta'addanci saboda 'yan adawa ne."
"Babu wani dan Najeriya da zai saka wadannan makudan kudi a ta'addanci, yanzu an ce wasu na daukar nauyin ta'addanci saboda rashin jituwa a tsakaninsu."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan farmaki Zamfara, sun halaka masu azumi da dama

- Ahmed Gumi

Gumi ya ce an san maboyar 'yan bindiga

A wani labarin mai kama da wannan, Sheikh Ahmed Gumi ya ce jami'an tsaro sun san maboyar 'yan bindiga a Arewacin Najeriya.

Gumi ya ce tare suke zuwa da wasu daga cikin jami'an tsaron wurin 'yan ta'addan lokacin da ya ke jagorantar sulhu.

Wannan na zuwa ne yayin da malamin ke kiran gwamnati da ta yi sulhu da 'yan bindiga domin kawo karshen matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.