Siyasar Kano: Kwankwaso na nan daram-dam a APC - Aminu Dabo

Siyasar Kano: Kwankwaso na nan daram-dam a APC - Aminu Dabo

- Kwankwaso yana nan daram a APC inji Aminu Dabo

- Ya ce karya da jita - jitar mutane ce kawai da ake cewa zai bar APC

- An bawa shugaban 'yan sanda umarnin karfafa tsaro a duk lokacin da Kwankwaso zai kai ziyara Kano

Siyasa: Kwankwaso na nan a APC - Aminu Dabo
Siyasa: Kwankwaso na nan a APC - Aminu Dabo
Asali: Facebook

A jiya litinin ne, wani makusanci ga tsohon gwamnan Kano wato Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Architect Aminu Abubakar Dabo, ya karyata jita - jitar da ake yi na cewar Sanata Kwankwason ya bar jam'iyyar APC.

Da yake jawabi ga manema labarai a Kano, Dabo ya ce Sanata Kwankwaso har yanzu yana nan a jam'iyyar APC, ya ce jita - jita ce kawai mutane ke yada wa, cewar ya bar jam'iyyar, wanda hakan ba gaskiya bane,

DUBA WANNAN: Kwallon kafa: Najeriya tasha kashi a gasar zakarun Afrika

"Ya ce lallai ne muna halartar tarurruka, wanda hakan al'adace ta kawonne dan siyasa. Ya ce kamar yadda ake ta fada muna yin taro saboda muna son sauya sheka, wannan maganar ba gaskiya ba ce.

Ya kara da cewar Kwankwaso zai zo Kano nan ba da dadewa ba, za a saka ranar zuwan shi da zarar majalisar datijjai sun ba da dama.

Ya jaddada cewar kwankwaso na nan daram a jam'iyyar APC, ba gudu ba ja da baya, saboda bai kamata ace an fara samun baragurbi a cikin jam'iyyar ta APC ba.

Sannan majalisar dattijai ta ba wa babban Sufeton 'yan sanda ya karfafa tsaro a duk lokacin da Sanata Kwankwason zai shiga kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: