'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Jami'an Tsaro a Arewa, Sun Halaka Mutum 4

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Jami'an Tsaro a Arewa, Sun Halaka Mutum 4

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Yantumaki da ke ƙaramar hukumar Danmusa ta jihar Katsina
  • Miyagun ƴan bindigan sun halaka mutum ɗaya wanda jami'in rundunar 'Katsina Community Watch Corps' ne a yayin harin
  • Wasu ƴan bindigan sun kuma halaka wasu jami'an rundunar mutum uku a Unguwar Damari da ke ƙaramar hukumar Sabuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Wasu ƴan bindiga biyar da sanyin safiyar jiya sun kai wani mummunan hari a Yantumaki cikin ƙaramar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina.

Ƴan bindigan sun kai hari ne gidan wani Malam Suleiman Mai Rake da ke Unguwar Yayyara a Yantumaki, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da 'mata 55' ƴan rakon amarya ɗaki a jihar Arewa

Yan bindiga sun halaka jami'an tsaro a Katsina
'Yan bindiga sun kai farmaki kan jami'an tsaro a Katsina Hoto: Dr. Dikko Umar Radda
Asali: Twitter

Mutumin, wanda aka ce shi ne mahaifin Isa Bawa Yantumaki, wanda jami'in rundunar tsaro ta 'Katsina Community Watch Corps' ne, ya rasa ransa a yayin farmakin, inda maharan suka yi awon gaba da shanunsa guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun halaka wasu jami'an rundunar

Tun da fari dai, da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Juma’a, wasu gungun ƴan bindiga ɗauke da babura bakwai wadanda ake kyautata zaton daga dajin Madachi ne, suka kai hari Unguwar Damari a ƙaramar hukumar Sabuwa.

A yayin harin sun kashe Shehu Armaya’u ɗaya daga cikin jami’an tsaro na Katsina Security Watch Corps da wasu mutum biyu, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Majiya mai tushe ta bayyana cewa Armaya’u wanda a kwanakin baya ya samu izinin ziyartar iyalansa ya gamu da ajalinsa a harin.

A cewar majiyar, Armay’au da sauran mutum biyun da aka kashen, Lawal da Mamuda, duk sun fito ne daga ƙauyen Damari.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya sa a kama fitaccen malamin Musulunci a Arewa? Gaskiya ta bayyana

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, bai tabbatar da faruwar lamarin ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

An Halaka Tsohuwa da Jikarta a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagu sun shiga har cikin gida sun halaka wata tsohuwa da jikarta a garin Daura da ke jihar Katsina.

Miyagun maharan dai sun halaka mutanen ne a cikin wani yanayi mara daɗi bayan sun yi musu kutse cikin gidansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel