Jawabin Janar Dogonyaro yayin da suka yi wa Buhari juyin-mulki shekaru 36 da su ka wuce
- A ranar Alhamis ne Janar Joshua Dogonyaro ya rasu a asibitin UJTH
- Joshua Dogonyaro ne sojan da ya bada sanarwar juyin mulki a 1985
- Dogonyaro yana cikin wadanda suka kifar da Gwamnatin sojin Buhari
A karshen makon nan ne aka samu labari cewa Janar Joshua Dogonyaro mai ritaya ya rasu.
Joshua Dogonyaro wanda ya taba rike rundunar ECOMOG ta kasashen yammacin Afrika ya rasu ne a asibitin UJTH da ke garin Jos, ya na da shekara 80.
Jaridar The Cable ta kawo jawabin da Janar Joshua Dogonyaro ya yi bayan sun hambarar da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a Agustan 1987.
KU KARANTA: Mu kanmu, ‘Yan bindiga sun addabe mu - Mutanen Fulani
Marigayin ya na cikin wadanda su ka taya Janar Ibrahim Badamasi Babangida juyin-mulki, kuma ya yi jawabi a madadin sojojin da suka yi wa Buhari tawaye.
Mun tsakuro kadan daga cikin jawabin da tsohon sojan ya yi a lokacin da su ka yi juyin-mulkin:
“Ni Birgediya Joshua Nimyel Dogonyaro, na sojojin kasa, ina mai bada wannan sanarwa a madadin sauran abokan aiki na a gidan soja.”
“Al’ummar kasarmu, tsoma kan sojoji da su kayi cikin sha’anin mulki a karshen 1983 abin da aka yi farin ciki ne. ‘Yan Najeriya sun karbi sauyin, suna sa ran a samu cigaba. Bayan kusan shekaru biyu, ta nuna cewa burinsu ba zai cika ba.”
KU KARANTA: Hakurin 'Yan Najeriya ya sa Buhari yake cigaba da mulki – Adebanjo
“Saboda mutanen Najeriya da wadanda za su zo nan gaba, ba su da wata kasa ban da Najeriya, ba za mu tsaya zugum, muna kallon wasu tsiraru su cigaba da amfani da karfin mulki domin bukatar karon kansu, a maimakon daukacin al’umma.”
“Babu wata kasa da za ta iya samun cigaban kirki idan babu hadin-kai tsakanin manyan gwamnati…"
“Ya bayyana karara, kasa za ta shiga cikin hadari idan aka cigaba da sakin layi. Muna fuskantar wannan kalubale. A irin wannan yanayi, idan za a iya daukar mataki, hakan ya kamata, shi ne abin da mu ka yi.”
A ranar Juma'a ne aka ji cewa Gwamna Simon Lalong ya ce marigayi Joshua Dogonyaro ya bashi shawarwari a kan hanyar da za a shawo kan matsalar tsaro.
Gwamnan jihar Filato ya aika da ta'ziyyarsa, yayi addu'ar samun rahamar Ubangiji ga marigayin, tare da samun juriya ga iyalansa na wannan babban rashin.
Asali: Legit.ng