An Bankado Manyan Mutanen Dake Daukar Nauyin Ta’addanci a Najeriya – Malami

An Bankado Manyan Mutanen Dake Daukar Nauyin Ta’addanci a Najeriya – Malami

- Nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wasu ‘yan Najeriya kan kasancewa da hannu a cikin ayyukan da suka shafi ta’addanci

- Ba kowa bane ya bayyana wannan sai Babban Atoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami

- Sai dai kuma, Ministan bai bayar da sunan kowa ba

Fitattun ‘yan Najeriya wadanda ke daukar nauyin ta’addanci za su fuskanci tsarin shari’a nan ba da jimawa ba kasancewar gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen gurfanar da su.

Babban Atoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami (SAN) ne ya bayyana wannan ci gaban a ranar Juma'a, 7 ga watan Mayu, jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Kamata Yankin Kudu Maso Gabas Ya Yi Don Lashe Shugabancin 2023

An Bankado Manyan Mutanen Dake Daukar Nauyin Ta’addanci a Najeriya – Malami
An Bankado Manyan Mutanen Dake Daukar Nauyin Ta’addanci a Najeriya – Malami Hoto: @MalamiSan
Asali: Twitter

Malami wanda bai bayyana sunayen wadanda ake zargin ba ko kuma yawan mutanen da abin ya shafa ba ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, in ji jaridar The Cable.

Ya ce:

“Wani lokacin can baya, akwai wasu hukunce-hukuncen da aka yanke wa‘ yan Najeriya da ake zargi da hannu a cikin ayyukan ta’addanci a Hadaddiyar Daular Larabawa.

“Ina mai farin cikin bayar da rahoton cewa an dade ana gudanar da bincike kuma ya kai wani mataki na ci gaba.

“Tashi daga binciken, akwai, tabbas, akwai dalilai masu ma'ana na zato cewa yawancin 'yan Najeriya, manyan mutane, hukumomi, da sauran su, suna da hannu a daukar nauyin ta'addanci kuma an gabatar dasu don gurfanar dasu.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da marigayiya Aisha Alhassan, Mama Taraba

“A zahiri, gaskiya ne cewa gwamnati tana tuhuma kuma hakika ta fara shirya matakai na gurfanar da wadannan manyan mutane da aka gano suna tallafawa ta'addanci. Gaskiya ne.”

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta abinda ya kwatanta da 'rashin tausayin wasu 'yan Najeriya' ga cigaba, inda yayi kira ga 'yan kasa da su dinga dubawa kasar nan.

Buhari ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a yayin da yake jin bayani daga PEAC wacce Farfesa Doyin Salami ke jagoranta, a taronta na 6 a gidan gwamnati dake Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel