Za a Dakatar da Ba Tsofaffin Gwamnoni da Mataimakansu Kudin Fansho, an Samu Bayani
- Majalisar dokokin jihar Abia ta amince da kudirin dokar da ta dakatar da tsofaffin gwamnoni da mataimakansu daga karbar kudin fansho
- Tun da fari, dan majalisa mai wakiltar mazabar Arochukwu, Mr. Uchanna Okoro ya gabatar da kudirin a gaban majalisar domin amincewa
- Yayin da ya ke sanar da na'am da dokar, kakakin majalisar, Emmanuel Emeruwa ya ce dokar za ta rage kashe kudaden gudanar da mulki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Abia - A ranar Talata ne majalisar dokokin jihar Abia ta zartar da kudirin dakatar da biyan kudaden fansho ga tsofaffin gwamnoni da mataimakansu a jihar.
An yi wa dokar taken: “Kudirin dokar (H.A.B 11:) don soke dokar fansho ta gwamnoni da mataimakan gwamnonin jihar Abia ta 2001 da sauran batutuwan da suka shafe ta.”
Manufar soke fanshon gwamnoni a majalisa
Rahoton Premium Times ya nuna cewa, Uchanna Okoro, shugaban masu rinjaye kuma mai wakiltar mazabar Arochukwu ne ya fara gabatar da kudirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin majalisar jihar, Emmanuel Emeruwa, ya sanar da amincewa da kudirin bayan karatu na daya, na biyu, da kuma karatu na uku yayin zaman majalisar.
Mista Emeruwa, yayin da yake taya ’yan majalisar murna, ya ce dokar za ta rage kashe kudin gudanar da mulki a jihar.
"Dokar za ta fara aiki nan take" - Majalisa
The Cable ta ruwaito cewa dokar da zarar gwamnan ya amince da ita za a kira ta da "Dokar gwamnoni da mataimakan gwamnonin jihar Abia (da aka sabunta) a 2024."
Shugaban majalisar ya ce sabuwar dokar fansho ga gwamnoni za ta fara aiki nan take bayan gwamnan ya sanya hannu a kanta.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, da wannan sabuwar dokar, tsofaffin gwamnoni da mataimakansu za su daina karbar fansho bayan karewar wa’adinsu.
Majalisa na neman ministan Tinubu
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa majalisar wakilai ta gayyaci ministan lafiya Farfesa Mohammed Ali Pate da ya bayyana gabanta domin amsa tambayoyi.
Majalisar na zargin ma'aikatar lafiya ta fitar da $300m domin yaki da zazzabin cizon sauro a 2021, sai dai ta gano akwai lauje cikin nadi a yadda aka kashe kudin.
Hakazalika majalisar ta yi barazanar yin amfani da karfin ikonta na kama babbar sakatariyar ma'aikatar, wadda ta ki amsa gayyatar majalisar har sau uku.
Asali: Legit.ng