Kamar Legas, Kwara za ta dena biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu fansho
- Gwamnatin Jihar Kwara zata dena biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu kudin fansho a jihar Kwara
- Wannan matakin ya yi kama da irin wadda gwamnatin Jihar Legas ta dauka a baya bayan nan
- Gwamnan Jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba
Gwamnatin Jihar Kwara zata soke dokar biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu kudaden fansho kamar yadda gwamnan jihar ya sanar a shafinsa na Twitter.
Wannan matakin ya yi kama da wadda gwamnatin Jihar Legas ta dauka a baya bayan nan inda ta ce za ta dena biyan tsaffin gwamnonin da mataimakansu kudaden fansho.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun sace wasu da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja
Gwamna Abdulrazak yace jihar na bukatar kudade don inganta rayuwar al'ummar jihar, inda ya ce ya yi imanin zai fi dacewa ayi amfani da kudaden jihar wurin magance talauci da samar wa matasa ayyukan yi.
KU KARANTA: Cibiyar Lafiya ta ce ana fuskantar karancin kororon roba a wani gari a Bauchi
A bangarenta, gwamnatin na Legas ta ce ta dauki matakin ne don rage kudaden da gwamnatin jihar ke kashewa a kansu don ta mayar da hankali kan yin ayyukan da zasu inganta rayuwar 'yan jihar.
Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam'iyyar APC na kasa, Ahmed Bola Tinubu a martanin da ya yi ya ce yana goyon bayan matakin da gwamnatin na Legas karkashin jagorancin Gwamna Babajide Sanwo-Olu ta dauka.
A wani labarin daban, kun ji gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, ya gaya wa shugabancin jam'iyyar PDP a Abuja ranar Talata cewa zai bar jam'iyyar.
Ya ce zai koma jam'iyya mai mulki ta APC yana mai ikirarin cewa APC zata bawa dan yankin sa na kudu maso gabas takara a zaben 2023.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng