Jerin Jihohin Najeriya da ke da dokar biyan Gwamnonin-baya fansho
A halin yanzu an tado da maganar biyan tsofaffin gwamnonin Najeriya makudan kudi da sunan fansho. Tsofaffin mataimakan gwamnonin wadannan jihohi su kan amfana da wannan fansho.
Binciken da BudgetIT ta yi, ya nuna cewa jihohi 23 su ke da wannan doka ta ba gwamnonin baya miliyoyin kudi duk wata. Ana wannan hidima ne duk da irin tulin gatar da dokar kasa ta yi masu.
Jihohin da su ke da dokar biyan tsohon gwamna da mataimakinsa kudin fansho su ne:
1. Bauchi
2. Ribas
3. Akwa Ibom
4. Legas
5. Sokoto
6. Gombe
7. Yobe
8. Kwara
9. Abia
10. Osun
11. Edo
12. Imo
13. Delta
14. Kano
15. Jigawa
16. Oyo
17. Niger
18. Bayelsa
19. Katsina
20. Ondo
21. Borno
22. Anambra
23. Ebonyi
KU KARANTA: Ana wasan tonon silili tsakanin Yari da gwamna Matawalle
Hakan na nufin gwamnonin da su ka mulki a jihohin Adamawa, Benuwai, Kuros-Riba, Ekiti, Enugu, Kebbi, Kogi, Nasarawa, Ogun, Filato da Taraba, ne kurum ba su samun wannan kudi.
A farkon shekarar 2017, Jaridar Vanguard ta yi wani bincike inda ta gano cewa ana kashe fiye da Naira biliyan 37 a matsayin fansho na tsofaffin gwamnonin jihohin da su ka yi mulki a kasar.
Kawo yanzu wannan kudi ya karu sosai ganin an yi zabubbuka a jihohi da-dama inda har an samu sauyin gwamnati a irinsu Oyo, Ogun, Ondo, Ekiti, Kwara, Bauchi, da Adamawa bayan nan.
Daga cikin jihohin da su ka fi ko ina kashe wannan kudi akwai Bauchi, Ribas, Akwa Ibom da Legas. Bugu-da-kari wasu tsofaffin Gwamnonin sun zama Sanatoci ko Ministocin gwamnati.
Wadanda su ka yi mulki su kan kuma tashi da sababbin motoci bayan ‘yan shekaru tare da gidaje a gida da Abuja. Bayan samun damar tafiya hutu a ketare da kuma ganin Likita bini-bini.
Ganin yadda ake batar da kudi a kan gwamnoni yayin da al’umma su ke cikin wani hali ne ya sa gwamnatin Zamfara ta soke wannan doka, ta haramtawa tsofaffin gwamnoni samun fansho.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng