Ramadan: Matakin da Ƴan Sandan Kano Suka Ɗauka Kan Wasannin ‘Tashe’
- Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gargadi matasa da su guji tada zaune tsaye a a lokacin gudanar da wasannin al’ada na tashe
- Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usaini Gumel ne ya yi wannan gargadin a yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na Kano
- Gumel ya ce rundunar ‘yan sanda ta dukufa wajen tabbatar da tsaro ga daukacin al’ummar Kano a tsawon watan Ramadan da bayansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a ranar Litinin ta gargadi matasa da su guji tada zaune tsaye a cikin watan Ramadan, musamman a lokacin gudanar da wasannin al’ada na “tashe”.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ana fara gudanar da wasannin 'tashe' ne a tsakiyar watan Ramadan mai alfarma kuma a kammala a sa'o'i kadan kafin a fara bukukuwan Sallah.
Yan sandan Kano sun kira taron tattaunawa
'Tashe' wata al'ada ce da ake shiryawa a cikin watan Ramadan inda mutane musamman matasa maza da mata ke nuna wasu nau'ika na al'adun Hausa ta hanyar barkwanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu matasa suna amfani da al'adar tashe wajen tayar da tarzoma ga mazauna garin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usaini Gumel ne ya yi wannan gargadin a yayin wani taron tattaunawa da sarakunan gargajiya na jihar Kano.
Haka zalika, akwai shugabannin al’umma, hukumomin addini da kuma manyan matasan jihar, a cikin mahalarta taron wanda ya gudana a ofishin ‘yan sanda na Bompai, Kano.
Kano: Matakan da 'yan sanda suka dauka
Jaridar The Punch ta rahoto Gumel ya ce a cikin matakan da rundunar ta dauka, akwai kara sanya ido da yawan sintiri a yankunan da aka gano matasa na amfani da al’adar Tashe don aikata munanan ayyuka.
"Muna da tabbacin cewa wannan taron zai wayar da kan jama'a game da hatsarin da ke tattare da yin ayyukan da ke lalata zaman lafiyar jama'a.
“Rundunar ‘yan sanda ta dukufa wajen tabbatar da tsaro ga daukacin al’ummar Kano a tsawon watan Ramadan da bayansa."
Kwamishinan ya kuma yi kira ga mazauna Kano da su kara sanya ido tare da gaggauta kai rahoton duk wani mai yunkurin tayar da tarzoma ga hukumomin tsaro domin daukar mataki.
2023: Dakatar da al'adar tashe a Kano
Ko a lokacin azumin 2023, Legit Hausa ta ruwaito yadda rundunar 'yan sandan jihar Kano ta haramta yin wasannin tashe kwata kwata a jihar.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Haruna Kiyawa ne ya sanar da matakin rundunar na haramta tashe a jihar saboda yunkurin wasu bata gari na tayar da zaune tsaye.
Kiyawa ya kuma sanar da haramcin yin wasannin kilisa da wasan wuta, inda ya ce rundunar za ta dauki mummunan mataki kan wadanda suka saɓa wannan umarni
Asali: Legit.ng