Gwamnatin Katsina ta Gaggauta Haramta Wasannin 'Tashe' da Ake a Ramadana

Gwamnatin Katsina ta Gaggauta Haramta Wasannin 'Tashe' da Ake a Ramadana

- Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana sanarwar haramta Tashe da ake gudanarwa a Ramadana

- Gwamnatin jihar ta bayyana dalilan da yasa ta yanke shawarin haramta wasannin na Tashe

- Hakazalika ta yi kira ga iyaye da su kula yaransu su tabbatar da cewa an bi dokar cikin lumana

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ya hana wasan Tashe na gargajiya da ake gudanarwa a cikin watan Ramadan, gidan talabijin Channels ya ruwaito.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, al'adu, da harkokin cikin gida, Abdulkarim Yahaya Sirikathe ya fitar, haramcin na zuwa ne kwanaki 15 kacal bayan fara azumin Ramadana biyo bayan wasu rahotannin tsaro da suka jawo hakan.

Gwamnatin jihar ta kuma umarci jami'an tsaro a jihar da su kamo duk wanda aka samu da keta umarnin.

Kwamishinan ya ja hankalin Jama'a galibi iyaye kan bukatar kula da kiyaye 'ya'yansu don kada su gudanar da wasannin Tashe a duk fadin jihar.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: ’Yan Bindiga Sun Bankawa Babbar Kotun Tarayya Dake Ebonyi Wuta

Gwamnatin Katsina ta Gaggauta Haramta Wasannin 'Tashe' da Ake a Ramadana
Gwamnatin Katsina ta Gaggauta Haramta Wasannin 'Tashe' da Ake a Ramadana Hoto: bbc.com
Asali: UGC

“Anan ne Gwamnatin Jihar Katsina ke sanar da cikakken dokan hana wasannin Tashe na gargajiya wadanda galibi ake gudanarwa a cikin watan Ramadana.

“Gwamnan jihar Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya bada umarnin dakatarwar ne biyo bayan wasu rahotanni na tsaro.

"Don haka, muna fata mutane za su ji kuma su bi wannan umarnin, don Allah." Sanarwar ta kara da cewa.

KU KARANTA: Za Mu Dauki Mataki Kan Duk Wanda Yake Watsa Hotunan Sojoji da Aka Kashe, Gidan Soja

A wani labarin daban, Bisa al’da da zaran an kai azumi 10 na farko, kananan yara da ma wasu manya kan fita yin wasannin barkwanci da sunan tashe, inda za a dunga basu kyaututtuka.

Sai dai a jihar Kano wadda take a matsayin daya daga cikin manyan yankuna na kasar Hausa, abin ya sha bambam.

Domin kuwa kamar yadda ta faru a wasu shekarun baya, a wannan karo ma hukumomi a jihar sun haramta gudanar da wannan al'ada mai dinbin tarihi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.