Rundunar Yan Sanda Ta Haramta Al'adar Tashe a Jihar Kano Saboda Tsaro

Rundunar Yan Sanda Ta Haramta Al'adar Tashe a Jihar Kano Saboda Tsaro

  • Hukumar yan sanda ta haramta wasannin Tashe da ake yi a watan Azumin Ramadan a jihar Kano
  • Kakakin hukumar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an hana Tashe ne saboda gurbatattu na badda kama su aikata mugun nufinsu
  • Ya kara jaddada haramci kan hawan kilisa da wasan wuta, ya ce duk wanda aka kama zai ɗandana kuɗarsa

Kano - Rundunar 'yan sanda reshen jihar Kano ta sanar da cewa ta dakatar da al'adar nan da aka saba yi a watan Ramadana watau 'Tashe' a cikin kwaryar birni.

Tashe wata al'ada ce ta barkwanci da Malam Bahaushe ya saba gudanarwa daga ranar 10 ga watan Ramadana har zuwa karshe, kamar yadda Daily Trust ra rahoto.

Wasannin Tashe
Rundunar Yan Sanda Ta Haramta Al'adar Tashe a Jihar Kano Saboda Tsaro Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

A tsakanin wannan lokacin, Musulmai musamman kananan yara da matasa masu tasowa kan yi shiga daban-daban suna zuwa gida-gida su rera wakokin tashe.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Sansanin Yan Gudun Hijira a Arewa, Sun Kashe Mutane Sama da 40

Masu tashe na shiga gida-gida da majalisar jama'a da wurin sana'o'i su rera wakokin barkwanci da ka kirkira musamman don Tashe kuma akan ba su 'yan kuɗi da basu taka kara sun karya ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan sanda sun haramta Tashe a cikin birni

Sai dai hukumar yan sanda ta bakin jami'in hulɗa da jama'a reshen Kano, SP. Abdullahi Haruna Kiyawa, ta ce daga yanzu ta haramta wasan Tashe a faɗin jihar.

A cewarsa, abinda ya sa hukumar yan sanda ta hana Tashe shi ne saboda, "Masu aikata laifi na fakewa da sunan tashe su aikata laifuka kamar dabanci, fashin waya, fasadi da shan kwayoyi."

SP Kiyawa ya kara da cewa duk wanda ya sake aka damƙe shi yana saɓa wa wannan doka zai fuskanci fushin doka.

Bugu da ƙari, hukumar 'yan sanda ta jaddada haramcin hawan doki da ake kira Kilisa da kuma wasan hura wuta da ake yi, ta ce duk wanda ya saɓa za'a cafke shi kuma a hukunta shi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kwantan Bauna, Sun Kashe Da Dama

"Muna kira ga ɗaukacin al'umma su yi amfani da wannan lokaci mai daraja su yi wa Kano da ƙasa baki ɗaya addu'a, sannan kar su yi ƙasa a guiwa wajen kai rahoton motsin wanda ba su yadda da shi ba ga Caji Ofis mafi kusa," inji Kiyawa.

Ortom Ya Yi Ta'aziyyar Kashe Mutane 134, Ya Roki Buhari Ya Turo Sojoji

A wani labarin kuma Gwamna Samuel Ortom ya magantu kan hare-haren makiyaya da ya yi ajalin mutane sama da 100 a Benuwai

Gwamnan ya roki shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya aiwatar da kalamansa a aikace, ya ce abubuwa sun ƙara dagulewa a kananan hukumomi 3.

Asali: Legit.ng

Online view pixel