Kano: Yan Sanda Sun Kama Mutum 30 Kan Yunkurin ‘Tayar Da Tarzoma’ Yayin Auren Gata

Kano: Yan Sanda Sun Kama Mutum 30 Kan Yunkurin ‘Tayar Da Tarzoma’ Yayin Auren Gata

  • Yan sanda sun cafke mutane 30 da ake zargin suna yunƙurin kawo cikas a bikin Auren gata da aka yi ranar Jumu'a a Kano
  • Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Mohammed Gumel, ya ce mutanen sun bayyana abin da ya kawo su wurin ɗaura aure
  • Ya kuma buƙaci mutanen Kano su kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba ga hukumomin tsaro mafi kusa da su

Jihar Kano - Bayanai sun nuna akalla mutane 30 ne suka shiga hannu bisa zargin yunƙurin tada zaune tsaye yayin bikin 'Auren Gata' da aka yi kwanan nan a jihar Kano.

A ranar Jumu'a da ta gabata, gwamnatin jihar Kano ta ɗauki nauyin haɗa ma'aurata 1,800 a faɗin kananan hukumomin jihar guda 44, The Cable ta ruwaito.

An kama mutane 30 da suka so tada zaune tsaye a Auren gata na Kano.
Kwamishinan yan sanda ya bayyana nasarar da suka samu a bikin auren gata Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Baya ga haka, gwamnatin karƙashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta kuma biya sadakin N50,000 ga kowace amarya a madadin Anguna.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'an Tsaron Haɗin Gwiwa Sun Yi Artabu da Makiyaya, Ana Fargabar da Yawa Sun Mutu

Da yake jawabi a wata hira ranar Litinin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Gumel, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a yayin da biki ya kankama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun tatsi bayani daga mutanen

Gumel ya ce akasarin wadanda ake zargin sun fito ne daga jihohin makwabta da shirin kawo cikas a bikin auren gata, yayin da wasu suka halarci daurin auren saboda su yi sata.

A rahoton Vanguard, CP ya ce:

“Ina tabbatar muku cewa ana zaune lafiya a Kano kuma za a ci gaba da zaman lafiya. Yayin daurin auren gata da aka yi a karshen mako, wasu sun so tada tarzoma, amma ba mu bari hakan ta faru ba."
"Mun kama mutane 30 da suka zo da nufin kawo cikas ga taron. Da aka titsiye su, mun gano cewa yawancinsu sun fito ne daga jihohi makwabta. Wasu sun zo da mkulli da nufin satar motoci amma muka daƙile su."

Kara karanta wannan

Gwammatin Tinubu Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Mutane Aikin N-Power Na 2023? Gaskiya Ta Bayyana

"Kun ga yadda muka sami damar kare rayuka da dukiyoyi yayin babban taron. Babu wanda ya koka; wato mu nuna muku cewa muna kan turba”.

Ya kuma yi kira ga ɗaukacin al'umma su ci gaba da harkokin su na yau da kullum ba tare da fargaba ba, inda ya ce, "Kano na zaune lafiya."

Kwamishinan 'yan sandan ya buƙaci Kanawa da su kai rahoton duk wanda ba su gamsu da shi ba ga hukumomin tsaro a dukkan kananan hukumomin jihar 44.

Jami'an Tsaron Haɗin Guiwa Sun Yi Artabu da Makiyaya

Kuna da labarin cewa Jami'an tsaron Amotekun, OPC, da wasu ƙarin biyu sun yi gumurzu da Fulani makiyaya a jihar Oyo.

Rahoto ya nuna Makiyaya nw suka tsokano faɗan kuma suka yi wa jami'an kwantan bauna, ana fargabar da yawa sun mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel