Gurɓatattun Ƴan Siyasar da Aka Zaɓa Ne Suka Jefa Ƴan Najeriya a Mawuyacin Hali – Jigon PDP

Gurɓatattun Ƴan Siyasar da Aka Zaɓa Ne Suka Jefa Ƴan Najeriya a Mawuyacin Hali – Jigon PDP

  • Jigon jam'iyyar PDP daga jihar Imo, Stanley Ekezie, ya dora alhakin mawuyacin halin da ake ciki a Najeriya a kan gurɓatattun ƴan siyasa
  • Sai dai ya ce laifin masu kada kuri'a ne da suka riƙa karbar omo da taliya da wasu ƴan kudi kalilan suna zabar wadanda ba su cancanta ba
  • Ekezie ya ce ba za a taɓa ganin wani sauyi ba har sai ƴan Najeriya sun daina sayar da ƙuri'un su sun koma zaɓar nagartattun shugabanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Imo - Stanley Ekezie, wani babban jigo a jam'iyyar PDP a jihar Imo, ya ce masu zaɓe ne suka jefa Najeriya a mawuyacin halin da take ciki yanzu.

Kara karanta wannan

An samu asarar rayuka bayan fusatattun sojoji sun kona gidaje a Bayelsa

Jigon PDP, Stanley Ekezie, ya fadi abun da ya jawo tsadar rayuwa a Najeriya
Stanley Ekezie ya dora laifin wahalar rayuwar da ake ciki a Najeriya kan masu zabe. Hoto: Stanley Ekezie
Asali: Facebook

"Ƴan Najeriya sun sayar da ƙuri'unsu" - Ekezie

The Cable ta ruwaito cewa Ekezie ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ƴan jarida a Owerri, babban birnin jihar Imo a ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ekezie ya kara da cewa ƴan Najeriya sun karɓi taliya, omo da kudi sun zabi gurɓatattun ƴan siyasa.

Ya ce:

"Ku ɗora laifin komai a kan masu kaɗa ƙuri'a a Najeriya, su suka jefa ƙasar a mawuyacin hali. Sun zabi a ba su wasu 'yan kudi a saye ƙuri'unsu."

"Ƴan Najeriya su kuka da kansu" - Ekezie

"A zaɓen da ya gabata, an samu rahotannin sayen kuri'u ba adadi, masu ƙada kuri'a na karbar omo da taliya suna zabar gurɓatattun ƴan siyasa."

- A cewar jigon PDP.

Ita ma jaridar Leadership ta ruwaito Ekezie na cewa bai kamata ƴan Najeriya su riƙa kukan tsadar rayuwa ba, tun da sun san laifin su ne.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da ƴan takara 2 da ƙusoshin APC kan muhimmin batu a Villa, bayanai sun fito

'Dan siyasar ya ce Najeriya ba za ta taɓa samun cigaba ba, ma damar ana zaɓar wadanda ba su cancanta ba suna mulkar jama'a.

Ekezie ya magantu kan matsalolin PDP

"Abubuwa za su ƙara tabarbarewa ma damar aka ci gaba da zaɓen gurɓatattun mutane a matsayin shugabanni.
"Zaben 2027 wata dama ce da ƴan Najeriya za su iya yin amfani da ita wajen zaɓar nagartattun shugabanni."

- A cewar Ekezie.

Da ya ke takaicin rikicin da ya mamaye PDP, Ekezie ya nemi mambobin jam'iyyar da su shawo kan matsalolin domin samun nasara a babban zaben 2027.

Tsadar rayuwa: "Yan Najeriya na mutuwa"

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito Mr. Phrank Shaibu ya yi ikirarin cewa 'yan Najeriya na mutuwa sakamakon tsare-tsaren gwamnatin Tinubu da suka haddasa tsadar rayuwa.

Mr. Shaibu ya ce babu wani alkairi da ke tattare da manufofin gwamnatin APC illa kara cusa bakin ciki da tashe-tashen hankaluna da har yau gwamnatin ta gagara magancewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.