Shin ko kun san wanene Babban Dogarin shugaba Buhari
A yayin da Kanal Muhammad Lawal Abubakar, Babban Dogari kuma amintacce ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika shekaru 45 a duniya, Legit.ng ta kawo ma ku dan takaitaccen tarihin sa tare da rawar da ya taka a fagen sana'ar sa.
Tamkar shugaba Buhari, Kanal Muhammad ya kasance shugaban Dalibai na makarantar Dakarun Soji ta Nigerian Military School (NMS) da ya halarta a tsakanin 1985 zuwa 19990, kuma an haifi Babban Dogarin ne a ranar 28 Maris, 1973 a yankin Wusasa na garin Zaria.
Amintaccen Dogarin ya fara karatun sa na Digiri a jami'ar Ahmadu Bello dake garin Zaria, wanda daga bisani ya watsar kuma ya tafi jami'ar Dakarun Soji ta Nigerian Defence Academy a shekarar 1992 inda ya yi karatun sa a fannin nazarin halittu watau Biological Sciences kuma ya zamto dakarun Soja.
Kanal Abubakar ya taka muhimmiyar rawar gani da nuna kwarewar sa a fagen aiki, inda ya samu kyaututtuka bila adadin tare da rike kujerun mukaman soji da dama.
KARANTA KUMA: Jam'iyyar PDP ta janye gudanar da taron ta na jihar Kano
Rahotanni sun bayyana cewa, Kanal Muhammad ya samu kyatuttukan girmamawa da kuma lambar yabo kimanin goma.
Amintaccen Dogarin ya ziyarci fiye da kasashe 40 na fadin duniy, kuma yana nan tare da matar sa Hajiya Fatima Musa da kuma diyar sa kwara guda, Aisha Nawal.
Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, satar wayar salula ta sanya wani almajiri ya rasa hannayen sa biyu a jihar Gombe.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng