Bana son mijina, tursasani akayi na aureshi - Uwargida mai neman saki a kotu
Wata uwargida, Hadiza Ibrahim, ta bukaci kotun Shari’a da ke Zaune a Minna ta soke aurenta da mijinta saboda bata son shi.
Hadiza Ibrahim ta bayyanawa kotu cewa ta gargadi mijin tun daga fari cewa wannan auren dolen da akayi ba zai haifar da da mai ido ba.
“Ina rokon wannan kotu ta kashe wannan aure saboda bana son mijina.
“Na gargadeshi tun daga farko da shi da mahaifina suka tursasani cewa wannan aure ba zai dade ba.
“Auren dole ne kuma menene amfanin auren da bani son wanda nike aura.
“Babu abinda zai mayar dani gidansa, ko da ko yayi kokari wajen sasanta tsakaninmu."
KU KARANTA: Kwamitin sulhun jam'iyyar APC: Bakin alkalami ya riga ya bushe - Jigo a jam'iyyar APC
Amma shi mijin mai suna Aliyu ya bayyana cewa shi fa har yanzu yana son matarshi kuma baya son su rabu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng