Kisan Sojoji 16: Gwamnan PDP Ya Yi Martani Kan Harin, Ya Fadi Abin Da Zai Yi Kan Lamarin
- Yayin da aka kai hari da ya yi ajalin sojoji akalla 16 a jihar Delta, Gwamna Sherrif Oborevwore ya yi martani
- Gwamna Sherrif ya yi Allah wadai da harin da wasu bata gari suka kai kan sojojin a kauyen Okuama da ke jihar
- Gwamnan ya yi alkawarin bin dukkan hanyoyi da suka dace domin zakulo wandanda ake zargi tare da hukunta su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Delta - Gwamna Sherrif Oborevwore na jihar Delta ya yi Allah wadai da kisan sojoji a jihar.
Gwamnan ya tura sakon jaje ga iyalan sojojin da suka rasa rayukansu yayin harin da wasu bata gari suka kai.
Sanarwar da Gwamna Sheriff ya fitar
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Festus Ahon ya fitar, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce gwamnan ya kadu da matakin da mutanen kauyen Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu suka dauka.
"Gwamnatin jihar Delta ta kadu da kisan sojoji a jihar wanda hakan ya sabawa al'adun mutanen Delta."
"A madadin gwamnati da al'ummar jihar, ina mika sakon jaje ga iyalan wadanda suka mutu da kuma rundunar sojin baki daya."
"Gwamnatin jihar za ta bi dukkan hanyoyin da suka dace domin kamo wadanda ake zargin tare da fuskantar fushin hukuma."
- Sherrif Oborevwore
Kisan sojoji 16 da aka yi a jihar Delta
Sherrif ya kuma bukaci al'ummar jihar da su kasance masu bin doka domin tabbatar da zaman lafiya a jihar, Cewar Leadership.
Wannan na zuwa ne bayan kisan sojoji 16 a kauyen Okuama da ke jihar inda lamarin ya jawo Allah wadai daga ɓangarorin kasar.
A wasu rahotannin an tabbatar da cewa sojoji 22 suka mutu bayan harin da bata garin suka kai kan sojojin.
An kona kauyen da aka hallaka sojoji
Kun ji cewa ana zargin wasu fusatattun sojoji sun kona kauyen Okuama kurmus da safiyar yau Lahadi 17 ga watan Maris.
Kauyen Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a nan ne wasu bata gari suka kai hari kan sojoji tare da yin ajalinsu.
Asali: Legit.ng