Bayan Rage Farashin Abinci, Gwamnan APC Ya Lissafo Kasuwannin da Za a Iya Samun Kayan Cikin Sauki

Bayan Rage Farashin Abinci, Gwamnan APC Ya Lissafo Kasuwannin da Za a Iya Samun Kayan Cikin Sauki

  • Yayin da ake fama da tsadar kayan abinci a jihar Legas, gwamnatin jihar ta bude kasuwanni da za a siyar da kaya mai sauki
  • Gwamnatin ta shirya bude kasuwannin ne a yau Laraba 17 ga watan Maris domin samun saukin siyan kayan abincin
  • Wannan na zuwa ne bayan daukar matakin rage farashin kayan abincin da kaso 25 da gwamnan jihar ya yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Gwamnatin jihar Legas ta shirya bude kasuwanni da al'ummar jihar za su samu kayan abinci kan farashin mai sauki.

A yau Lahadi 17 ga watan Maris gwamnatin ta shirya bude kasuwanni da za a samu farashin cikin sauki da kaso 25.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya tona asirin inda aka kai daliban da aka sace a Kaduna, bayanai sun fito

Gwamnati ta lissafo kasuwannin da za suyi abinci cikin farashi mai rahusa
Gwamnatin jihar Legas ta fara siyar da kayan abinci cikin farashi mai rahusa. Hoto: Nurphoto.
Asali: Getty Images

Kayan abincin da za a samu sauki a Legas

Kwamishinan yada labaran jihar, Gbenga Omotosho shi ya tabbatar da haka inda ya ce Gwamna Babajide Sanwo-Olu ne ya ba da umarnin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Omotosho ya lissafi kayan abincin da ragin ya shafa kamar haka, wake da shinkafa da garri da tumatar da tattase da kwai da biredi da sauransu.

Har ila yau, ya ce an dauki matakai domin tabbatar da cewa an siyar da kayan abinci yadda ya dace ba tare da matsala ba.

Ya kara da cewa za a siyar da kilo 5 na shinkafa a farashin N5.325 yayin kilo daya kuma N1, 065, cewar Punch.

Sai kuma kilo biyar na wake kan farashin N6,225 yayin da kilo daya kuma zai kama N1,245.

Jerin kasuwannin da za a samu kayan abincin cikin rahusa:

Kara karanta wannan

An cafke babban lauya da zargin kin biyan 'yar gidan magajiya bayan sun gama lalata

1. Karamar hukumar Eti Osa – Makarantar Ikota, Lekki -Epe Expressway, Ikota.

2. Karamar hukumar Eti-Osa ta Gabas – kasuwar Admiralty Lekki Phase 1.

3. Karamar hukumar Ikoyi Obalende – Old Nursing Ground, 1-9 hanyar Awolowo, Ikoyi, cewar TheCable.

4. Ƙaramar hukumar Victoria Island – makarantar Victory Island Snr.

5. Karamar hukumar Lagos Island – makarantar Elegbata.

6. Karamar hukumar Lagos Island ta Gabas – makarantar Lafiaji.

Sauran kasuwannin da za a samu kayan

1. Karamar hukumar Ikorodu – makarantar Grammer ta Ikorodu, cewar The Nation.

2. Ƙaramar hukumar Igbogbo/Bayeku – makaranta Islamiyya ta Zumuratu.

3. Karamar Hukumar Ijede – makarantar Luwasa.

4. Karamar hukumar ljede Ikorodu ta Arewa.

5. Karamar hukumar Odogunyan Ikorodu ta Yamma – makarantar Cherubim and Seraphim.

6. Karamar hukumar Imota – makarantar karamar hukuma.

Kara karanta wannan

Matatar man Fatakwal za ta fara aiki yayin da Najeriya ke shirin daina shigo da fetur

7. Ƙaramar hukumar Imota Kosofe – makarantar St Emmanuel.

7. Karamar hukumar Ogudu Ikosi Isheri – makarantar Ikosi.

8. Karamar hukumar Ketu Agboyi Ketu – makarantar Comprehensive a Agboyi Ketu.

Sai kuma sauran kasuwanni da za a samu kayayyakin cikin sauki da dama da ke birnin Ikeja da Epe da kuma Badagry a jihar Legas.

Gwamna Sanwo-Olu zai rage farashin abinci

Kun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya shirya rage farashin abinci a kasuwanni.

Gwamnan ya tabbatar da daukar matakin ne yayin da ake cikin wani irin hali na tsadar rayuwa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel