'Yan fansho a jihar Gombe sun yi zanga-zanga a gidan gwamnati
- 'Yan fansho a jihar Gombe sun fito cincirindonsu don zanga-zanga kan rashin biyansu kudadensu
- Sun nemi haduwa da gwamnan jihar, sai da rahotanni sun bayyana baya gari a yayin zanga-zangar
- 'Yan fanshon sun samu ganawa da Sakataren gwamnatin jihar Fesfesa Ibrahim Njodi
Akalla mambobi dari uku na majalisar jihar Gombe na kungiyar 'yan fansho ta Najeriya a ranar Laraba suka toshe babbar kofar shiga gidan gwamnatin jihar ta Gombe lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa a yankin, jaridar Punch ta ruwaito.
A cewar Mohammed Abubakar, shugaban karamar hukumar a tattaunawar da yayi da manema labarai, yan fanshon suna zanga-zangar rashin biyansu kudaden fansho da ya kwashe watanni.
KU KARANTA: Abia: Muna biyan N100K kan duk wata saniya da aka kashewa makiyaya
"Sauran korafe-korafen da 'yan fansho ke yi shi ne cewa sama da masu ritaya na kananan hukumomi 700 ba a sanya su a cikin fanshon na wata ba bayan sama da shekaru biyu na ritaya tsakanin wasu da dama," in ji Abubakar.
Ya tabbata, an ga jami’an tsaro a kofar gidan Gwamnatin suna ta fafutikar tabbatar da doka da oda yayin da masu zanga-zangar lumana suka dage kan ganin Gwamnan.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, majalisar ta ci gaba da ganawa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Njodi a madadin Gwamnan wanda rahotanni ke cewa baya cikin jihar.
KU KARANTA: 'Yan fasa kwabrin shinkafar waje sun jikkata wasu jami'an Kwastam da wani soja
A wani labarin, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya nuna shirin gwamnatin jihar na kafa kwalejin addinin Musulunci da ke ba da difloma a kowace karamar hukuma 27 da ke fadin jihar.
Gwamnan ya bayyana shirin ne a jiya yayin bude taron jin ra’ayoyin jama’a na kwanaki uku kan cikakken gyaran tsarin koyar da ilimin addinin Musulunci na gargajiya, This Day ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng