Cushe a Kasafin 2024: PDP Ta Bukaci Akpabio Ya Yi Murabus, an Samu Karin Bayani

Cushe a Kasafin 2024: PDP Ta Bukaci Akpabio Ya Yi Murabus, an Samu Karin Bayani

  • Jam'iyyar adawa ta PDP ta yi kira ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya yi murabus daga mukaminsa
  • PDP ta yi wannan kiran ne yayin da take nuna goyon baya ga Sanata Abdul Ningi wanda majalisar ta dakatar kan kalamansa
  • Jam'iyyar hamayyar ta ce murabus din Akpabio ne kadai zai ba da damar yin bincike kan zargin Ningi na cewa an yi cushe a kasafin 2024

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A ranar Larabar nan ne jam’iyyar PDP ta bukaci Sanata Godswill Akpabio da ya gaggauta sauka daga kan kujerarsa ta shugaban majalisar dattawa.

PDP ta ce hakan ne kawai zai ba da damar a gudanar da bincike kan zargin cewa an yi cushen Naira tiriliyan 3.7 a cikin kasafin kudin 2024.

Kara karanta wannan

"Na karbi N266m": Abaribe, Ndume sun magantu kan ikirarin Ningi na cushe a kasafin 2024

Ningi: PDP ta nemi Akpabio ya yi murabus
PDP ta goyi bayan Sanata Ningi, tana so Akpabio ya yi murabus. Hoto: @Sen_AbdulNingi, @oficialGAkpabio
Asali: Twitter

Zarge-Zargen da PDP ke yi wa Akpabio

Jaridar Leadership ta rahoto daga wata sanarwa da Hon. Debo Ologunagba, sakataren yada labaran PDP ya fitar, jam'iyyar ta nemi Akpabio ya gaggauta mika kansa ga hukumar EFCC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar na magana ne a kan shari’ar da ake yi na zargin Akpabio ya wawure Naira biliyan 108 na al’ummar jihar Akwa Ibom a lokacin da ya ke matsayin gwamnan jihar.

“Bugu da kari kuma, ya kamata shugaban majalisar dattawa ya yi magana kan badakalar naira biliyan 86 na kwangilar da hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) ta yi a lokacin da yake rike da mukamin ministan harkokin Neja Delta.”

- Jam'iyyar PDPs

PDP ta goyi bayan Sanata Ningi

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa PDP ta kuma yi Allah-wadai da matakin dakatar da Sanata Abdul Ningi da majalisar ta yi ba tare da yin cikakken bincike kan batun cushe a kasafin kudin 2024 da ya ce an yi ba.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya hada kai da Atiku domin kirkirar sabuwar jam'iyya a 2027? Gaskiya ta fito

"Ya bayyana a fili cewa an dakatar da Sanata Ningi ne domin a rufe wata kafa ta bincike, wanda zai ba da damar boyewa gaskiyar abun da ya faru."

- Jam'iyyar PDP

PDP ta kara da cewa tana goyon bayan Ningi "saboda jajircewarsa wajen neman gaskiya da fadin ta komai dacin ta, tare da kuma rikon amanarsa a harkokin siyasa."

NSF: Sanata Ningi ya yi murabus

A wani labarin, Legit ta ruwaito cewa Sanata Abdul Ningi, ya yi murabus daga shugaban kungiyar sanatocin Arewa (NSF) biyo bayan dakatar da shi da aka yi daga majalisar dattawa.

Ningi a wasikar da ya aika wa kungiyar, ya bayyana cewa ba ya so rikicin da ake yi a majalisar ya shafi sanatocin na Arewa, kuma ya yi godiya ga sanatocin da suka bashi dama ya jagorance su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel