Ramadan: Hisbah Ta Aika da Muhimmin Gargadi Ga Wadanda Ba Musulmai Ba a Kano
- Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayar da sabon umarni ga waɗanda ba musulmai ba a jihar game da azumin watan Ramadan
- Darakta janar na hukumar Hisbah, Abba Sai’du ya yi kira ga waɗanda ba musulmai ba a jihar da su guji cin abinci a bainar jama’a
- Wannan umarnin dai na zuwa ne yayin da al'ummar musulmai a Najeriya da duniya baki ɗaya suka fara azumi a farkon makon nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta buƙaci wadanda ba musulmai ba da ba su yin azumi a wannan lokacin da su guji cin abinci a bainar jama'a.
Hukumar ta kuma gargaɗe su da su guji yin ayyukan da za su iya taɓa ƙimar addinin musulunci, cewar rahoton jaridar AIT Live.
Wane mataki hukumar Hisbah za ta ɗauka?
Jaridar Sahara Reporters ta ce Abba Sai’du, darakta janar na hukumar, ya bayyana cewa, jami'an hukumar za su ci gaba da gudanar da sintiri a birnin na Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a gudanar da sintirin ne domin cafke duk musulmin da aka samu yana gudanar da ayyukan da suka saɓa wa koyarwar addinin musulunci a cikin watan mai alfarma.
A cikin watan Ramadan dai musulmai suna ƙauracewa ci, sha, yin jima'i, da sauran abubuwan da aka haramta tun daga fitowar Alfijir har zuwa faɗuwar rana.
Idan ban da wurare irinsu Sabon Gari, Bompai da Jaba, mafi yawan wuraren da ake sayar da abinci a Kano a kulle suke da rana saboda azumi.
Al'ummar musulmai a Najeriya da sauran ƙasashen duniya sun fara azumin watan Ramadan na bana a ranar Talata, 10 ga watan Maris 2024, bayan an sanar da ganin jinjirin watan.
Hisbah ta cafke Murja Kunya a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah ta cafke fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, kan wasu zarge-zarge da ake yi mata.
Hukumar ƙarƙashin jagorancin Sheikh Malam Aminu Daurawa, ta cafke jarumar ne wanda ta shahar a manhajar ta TikTok, saboda kunnen uwar shegun da ta yi kan nasihar da aka yi mata.
Asali: Legit.ng