Za mu gina hanyar jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi – Shugaba Buhari
- Gwamnatin Buhari za ta gina hanyar jirgi zuwa cikin Kasar Nijar
- Yanzu haka Shugaban Kasar yace ana tattaunawa ne kan maganar
- Hanyar jirgin za ta ratsa tun daga Kano ya bi ta Daura har Maradi
A safiyar mu ka samu labari mai dadi a jawabin murnar shiga sabuwar shekarar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar inda yace za a fitar da hanya daga Najeriya zuwa Nijar. Dama dai ana cigaba da wasu aikin jirgin kasa a Najeriya.
Shugaban Kasar yace Gwamnatin sa za tana kokarin ganin ta shimfida hanyar jirgin Kasa ne daga Najeriya zuwa Kasar Jahmuriyyar Nijar. Za a tado aikin ne tun daga Jihar Kano zuwa Jihar Maradi da ke Nijar. Yanzu haka dai ana kan maganar ne.
KU KARANTA: Buhari ya koka da halin da rashin mai ya jefa wasu a Kasar
Hanyar jirgin da za ayi, zai faro daga Kano ne inda zai shiga Kazaure daga nan yayi Kasar Daura zuwa Garin Jibiya da ke kan iyaka a Jihar Katsina. Daga nan layin jirgin kasan zai tike a Jihar Maradi da ke cikin Kasae Jamhuriyyar Nijar.
Dama dai Shugaban Kasa Buhari yayi wannan jawabi ko kwanakin baya da ya kai ziyara Jihar Kano inda yace za a fara gyara hanyoyin cikin gida tukunna kafin a kai ga maganr jirgi zuwa Nijar. A bana dai za a ga tulin ayyuka a Kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng