Kotu Ta Haramtawa Magidanci Magana da Matarsa Na Tsawon Kwana da Kwanaki

Kotu Ta Haramtawa Magidanci Magana da Matarsa Na Tsawon Kwana da Kwanaki

  • Kotun Majistare da ke zama a Ado-Ekiti, jihar Ekiti, ta sanya takunkumi a kan wani magidanci mai shekaru 43 a duniya
  • Kotun ta ba da umurnin cewa ka da Chibike Nwakedi ya yi magana da matarsa, Blessing, har na tsawon makonni biyu
  • Alkalin kotun ya ce wanda ake karar zai iya magana da matarsa ne kawai ta hannun wani daga gefe, watau lauyanta

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Ekiti - Alkalin kotun majistare da ke zama a Ado-Ekiti, jihar Ekiti, ya umurci wani mutum mai shekaru 43, Chibike Nwakedi, da ka da ya yi magana da matarsa, Blessing na tsawon makonni biyu.

Mai shari'a Dolamu Babalogbon, ya ce kada wanda ake karar ya yi magana da matarsa kai tsaye ko ta hanyar kiranta a waya ko ma a kusa da ita, sai dai ta hannun lauyanta, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki tsattsauran hukunci kan likitan bogi da ake zargin ya kashe majinyaci

Alkalin kotu ya hana miji magana da matarsa
Alkali ya hana magidanci yi wa matarsa magana sai ya bi ta hannun wani Hoto: Court of appeal
Asali: UGC

Wani laifi mijin ya aikata?

Da ake gurfanar da shi, 'dan sanda mai gabatar da kara, sufeto Sodiq Adeniyi, ya fama ma kotun cewa wanda ake karar ya ci zarafin matarsa, Blessing Nwakedi, a ranar 3 ga watan Maris a Ado-Ekiti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adeniyi ya ce wanda ake zargin ya buga kafar matar na dama a jikin wani gadon katako, lamarin da ya kai ta ga samun gocewar 'kashi.

Sufeto Adeniyi ya kuma bayyana cewa a wannan rana, wanda ake karar ya yi abubuwa da ka iya tayar da zaune tsaye duk a wajen.

Ya kuma sanar da kotun cewa hukuncin abin da ya aikata yana nan a karkahin sashe na 189, 181 (D) da dokar laifuffukan jihar Ekiti 2021.

Kotu ta sa ranar ci gaba da shari'a

Lauya mai kare wanda ake kara, Barista Gbenga Ariyibi, ya bukaci kotun da ta bayar da belinsa, cewa ba zai tsallake sharadin beli ba kuma zai gabatar da wanda tsaya masa, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

"Ka canja mani rayuwa": Bature ya bai wa dalibin Najeriya naira miliyan 159 da sabuwar mota

Alkalin kotun ya bayar da belinsa kan kudi N50,000 da mutane biyu da za su tsaya masa sannan ya dage zaman zuwa ranar 28 ga watan Maris don ci gaba da sauraro.

Kotu ta warware auren shekaru 14

A wani labarin kuma, a ranar Talata ne wata kotu da ke Kubwa, Abuja, ta raba auren wata mata mai suna Salamatu Halilu da mijinta Ibrahim Sumaila bayan shafe shekaru 14 suna tare.

Alkalin kotun, Muhammad Wakili, ya raba auren ne kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada, bayan bukatar da Salamatu ta yi na neman saki bisa dalilin rashin soyayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng