Kaico: ‘Yan Sanda Sun Kama Magidanci Kan ’Dabawa’ Matarsa Wuka a Yobe

Kaico: ‘Yan Sanda Sun Kama Magidanci Kan ’Dabawa’ Matarsa Wuka a Yobe

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Yobe ta ce ta kama wani magidanci bisa zarginsa da kashe matarsa a gadon barcin ta
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim ya ce an kashe matar a ranar Alhamis, karfe 4:48 na yamma
  • Rahotanni sun bayyana cewa, lokacin da matar, Ammi Mamman ta mutu, mijinta Abubakar Musa na kwance a kan gadon

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Yobe - Rundunar 'yan sanda ta kama wani Abubakar Musa, bisa zargin sa da kashe matarsa, Ammi Mamman a garin Damaturu, jihar Yobe.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, kakakin rundunar, Dungus Abdulkarim, ya ce lamarin ya faru a ranar Alhamis, misalin karfe 4:48 na yamma.

Kara karanta wannan

An kama wata ‘kwararriyar’ barauniyar waya da wasu mutum 84 a Borno, ta bayyana yadda ta ke takunta

magidanci ya kashe matarsa a Yobe
Yan sanda sun kama magidanci kan ‘dabawa’ matarsa wuka a Yobe. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Yan sanda na kokarin gano bakin zaren mutuwar matar

Abdulkarim ya ce wanda ake zargin na kwance a gado daya da matar lokacin da aka daba mata wuka a wuya, wanda ya jawo zubar jini mai yawa, karshe ta mutu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce har yanzu rundunar na bincikar wanda ake zargin don gano bakin zaren yadda matar ta sa ta gamu da ajalinta a dakin barcin ta, The Cable ta ruwaito.

Peoples Gazette ta ruwaito rundunar na rokon duk wanda ke da masaniya kan lamarin ya matso kusa ya ba da rahoto don tabbatar da cewa an bi kadin ran matar da aka dauka.

Yan bindiga sun sace mata da miji da karamin yaro a Neja

A wani rahoton, 'yan binga sun shiga kauyen Garam da ke jihar Neja, inda suka yi harbin kan mai uwa da wabi, tare da sace miji da mata da wani yaro.

Kara karanta wannan

"Ruwan sama a Janairu": Mutane sunyi martani yayin da ruwan sama na farko ya sauka a Ibadan a 2024

Wani mazaunin garin, Mr Barnabas Lucky, ya shaida cewa 'yan bindigar sun kai harin ranar Talata, misalin karfe 12:13 na safiya.

Barnabas ya ce:

"Saboda harbe harben 'yan bindigar, ba mu iya yin bacci, mun tsorata sosai. Kuma wannan karo na biyu kenan da suke shigo wa garin namu."

Yan bindiga sun sako shugaban karamar hukumar Nasarawa

A wani lamarin makamancin wannan, 'yan bindiga sun sako Safiyanu Isah, shugaban karamar hukumar Akwanga da suka dace a kauyen Ningo.

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun sace Safiyanu tare da wani Alhaji Adamu a ranar 1 ga watan Janairu, 2024.

An ruwaito cewa sun nemi naira miliyan 10 kudin fansa, amma 'yan sanda sun ce ba a biya ko sisi ba har zuwa lokacin kubutar shugaban karamar hukumar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel