Emefiele Ya Cire Daloli Daga Asusu Babu Amincewar Buhari Ba, Fadar Shugaban Kasa

Emefiele Ya Cire Daloli Daga Asusu Babu Amincewar Buhari Ba, Fadar Shugaban Kasa

  • Fadar Shugaban kasa ta magantu kan yadda gwamnan CBN, Emefiele ya yi ta sha'aninsa tsawon shekaru takwas da Muhammadu Buhari ya yi yana mulki
  • Kakakin Shugaban kasa Bola Tinubi, Ajuri Ngelale ya ce Emefiele ya fitar da biliyoyin daloli daga asusun ajiyar kasar na kasashen waje ba tare da izinin Buhari ba
  • Ngelale ya ce tsohon shugaban babban bankin kasar yayi ta daukar wasu matakai ba tare da samun yardar tsohon shugaban kasar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Abuja - Kakakin Shugaban kasa Bola Tinubu, Ajuri Ngelale, ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, bai da masaniya kan tabarbarewar kudin ajiyar Najeriya na kasashen waje a karkashin kulawar tsohon gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele.

Kara karanta wannan

N585m: Jama'a sun taso EFCC da Tinubu a gaba saboda an ji tsit a binciken Edu

Emefiele wanda ke fuskantar shari’a a yanzu haka, shi ne ya ja ragamar CBN tsawon shekaru takwas da Buhari ya yi a karagar mulki.

Hadimin Tinubu ya yi karin haske kan badakalar Emefiele
Fadar shugaban kasa ta fadi yadda Emefiele ya fitar da biliyoyi ba da sanin Buhari ba Hoto: Muhammadu Buhari/CBN
Asali: Facebook

Koda yake tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya nada Emefiele bayan dakatar da Sanusi Lamido, Tinubu ya dakatar da shi ‘yan makonni bayan ya karbi mulki sannan ya bayar da umurnin bincikarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Emefiele: Babu amincewar Buhari aka fita da biliyoyi

A wata hira da aka yi da shi kwanan nan, Ngelale ya ce ba Buhari bane ya bayar da izinin cire biliyoyin daloli daga asusun kasar ba, wanda aka kashe a gwamnatin Emefiele, rahoton Daily Trust.

Ngelale ya ce Emefiele ya ci karansa babu babba ne saboda shine ke jan ragamar yawancin ayyukan CBN, rahoton Daily Post.

"Abubuwan da aka yi na kashe biliyoyin daloli daga asusun ajiyar kudin kasashen waje, an yi su ne ba tare da amincewa ko sanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaban kasa Bola Tinubu ba.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya tona asirin badakalar da Emefiele ya yi ba tare da sanin Buhari ba

"Eh, zai yi wuya wasu mutane su yarda da hakan, amma ina so na yi bayannin yadda hakan zai iya faruwa.
"Muna da daya daga cikin 'yan tsirarun Manyan Bankuna a duniya inda gwamnan babban bankin shi ne shugaban kwamitin daraktoci. Yana jan ragamar komai da kansa."

- Ajuri Ngelale

Me bincike ya nuna game da ayyukan Emefiele?

A gefe guda, mun ji cewa masanin binciken kwakwaf, Bamaiyi Haruna ya tabbatar da zargin yin amfani da saka hannun Buhari wurin kwashe $6.2m daga bankin CBN.

Haruna ya ce tabbas zargin da hukumar EFCC ke yi ya tabbata bayan gudanar da bincike mai zurfi kan takardun saka hannun.

Idan ba a manta ba hukumar EFCC ta yi zargin cewa an yi amfani da saka hannun Buhari da tsohon sakataren gwamnatin tarayya domin kwashe kudaden.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng