Hadimin Tinubu Ya Tona Asirin Badakalar da Emefiele Ya Yi Ba Tare da Sanin Buhari Ba

Hadimin Tinubu Ya Tona Asirin Badakalar da Emefiele Ya Yi Ba Tare da Sanin Buhari Ba

  • Yayin da wasu ke korafi kan mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, hadimin Tinubu ya bayyana abin da ya faru
  • Hadimin Shugaba Tinubu a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya ce akwai tsare-tsaren da aka yi a mulkin Buhari ba tare da ya sani ba
  • Ngelale ya zargi tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele da daukar wasu matakai da suka shafi ‘yan kasar ba tare da amincewar Buhari ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Hadimin Shugaba Tinubu a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya bayyana yadda aka lalata Najeriya a gwamnatin da ta gabata.

Ngelale ya ce tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya cire makudan daloli a asusun gwamnati ba tare da sanin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Kwastam ta ziyarci Buhari, sun yi magana kan bude iyakoki da Tinubu ke shirin yi

Hadimin Tinubu ya yi magana kan yadda Emefiele ya tarwatsa gwamnatin Buhari
CBN: Ngelale ya ce tsare-tsaren Buhari sun jefa jama'a cikin kunci. Hoto: Bola Tinubu, Muhammadu Buhari.
Asali: Twitter

Menene hadimin Tinubu ya ce kan Buhari?

Hadimin Shugaba Tinubu, Ngelale ya bayyana haka ne a cikin wata hira da dan jarida Jude Jideonwo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajuri ya ce da yawan abubuwan da Emefiele ya yi a lokacinsa, Mai girma Buhari bai ma san halin da ake ciki ba.

Ya ce tabbas zai yi wahala mutane su yarda amma an yi amfani da biliyoyin daloli ba tare da amincewar Buhari ba.

Ngelale ya koka kan yadda ake cikin kunci

“Abubuwan da aka yi na kashe biliyoyin kudade a lokacin Buhari an yi su ne ba tare da amincewarsa ba.”
“Wasu ayyukan bankin CBN da aka yi kamar daukar matakai kan tsarin kudade wanda gwamnan bankin ke da iko wanda kuma shi ne shugaban kwamitin darektoci.”
“Sauya fasalin Naira da ya jawo matsala a rayuwar al’umma, Emefiele ya shirya komai ba tare da duba matsalar hakan ga ‘yan kasa ba.”

Kara karanta wannan

Ka kula da lafiyarka madadin yawace yawace, Malamin addini ya ba Tinubu shawara

- Ajuri Ngelale

Ngelale ya kuma koka kan yadda ‘yan kasar da ba a taba kama su da laifin cin hanci ba amma suka shiga matsala saboda tsare-tsaren Emefilele.

Buhari ya yabi Tinubu

Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi magana kan mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Buhari ya yabawa Tinubu kan kokarin da ya ke yi inda ya ce wannan kasa ta na da wuyar sha’ani a lamarin mulki.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ta korafi kan salon mulkin Tinubu ganin yadda aka shiga mummunan yanayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel