Majalisa Ta Fara Binciken Gwamnatin Buhari Kan Kashe N200b a Shirin Kidayar 2023 da Aka Dakatar

Majalisa Ta Fara Binciken Gwamnatin Buhari Kan Kashe N200b a Shirin Kidayar 2023 da Aka Dakatar

  • Majalisar Wakilai za ta gayyaci babban daraktan hukumar kula da kidayar jama’a ta kasa (NPC) kan yadda aka kashe kudin kidayar 2023
  • A 2023, gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta fitar da kudi har N200b domin gudanar da kidayar jama'a da gidaje
  • Sai dai majalisar ta damu da yadda aka batar da kudin kudin alhalin Buhari ya dakatar da shirin kwanaki kadan kafin ya bar mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Majalisar Wakilai ta umurci kwamitinta kan kidayar jama'a da ya gudanar da bincike kan yadda aka kashe N200b a shirin kidayar shekarar 2023.

Majalisar ta umurci kwamitin da ya gayyaci babban daraktan hukumar kula da kidayar jama’a ta kasa (NPC) domin ya yi bayanin yadda aka kashe kudin.

Kara karanta wannan

Buga kudi: Yadda Buhari ya jawo hauhawar farashin kaya, Ministan Tinubu ya magantu

Zauren majalisar wakilai, Abuja
Majalisa za titsiye hukumar kidaya kan batar da N200b a 2023. Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

The Nation ta ruwaito cewa kwamitin zai bayar da rahoto a cikin makonni hudu domin ba majalisar damar daukar mataki kamar yadda doka ta tanadar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gwamnatin Buhari ta ware kudin shirin

Gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta shirya yin kidayar jama’a a shekarar 2022, amma daga baya ta dage shirin zuwa 2023.

A farkon watan Maris din 2023, tsohon karamin ministan kasafi da tsare-tsare na kasa, Clem Agba, ya ce za a bukaci jimillar N869b domin gudanar da aikin.

Premium Times ta ruwaito hukumar kididdiga ta kasa (NPC) ta ce, ta kashe kusan N200b a shirin yin kidayar jama’a da gidaje a shekarar 2023.

Honarabul Clement Akanni ya gabatar da kudirin

Sai dai Vanguard ta ruwaito cewa majalisar ta damu da yadda aka kashe kudin alhalin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da shirin kwanaki kadan kafin ya bar mulki.

Kara karanta wannan

BUK ta ba Abba Yusuf lambar yabo yayin da ilimi ya samu 30% a kasafin Kano a 2024

'Yan majalisa sun yanke shawarar gudanar da bincike kan shirin ne bayan amincewa da wani kudiri mai taken:

“Bukatar a binciki N200b da aka kashe kan kidayar jama’a da gidaje da aka dakatar a shekarar 2023,” wanda Honarabul Clement Akanni ya gabatar.

Kidayar 2023: An bar Tinubu jangwan - Sani

Tun da fari, Legit Hausa a watan Afrelu 2023, ta ruwaito Sanata Shehu Sani na cewa tsohon Shugaba Buhari ya bar Shugaba Bola Tinubu da nemo $1.8bn domin kirga jama'a da gidaje a kasar.

Shehu Sani ya bayyana hakan ne yayin da ya ke martani kan sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar na cewa Buhari ya dage shirin kidayar har sai nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.