Yayin da Aka Fara Azumi, Ma'aikatan NASU da SSANU Za Su Fantsama Yajin Aiki
- Yayin da aka fada azumin watan Ramadana, kungiyayon ma'aikatan Jami'o'i za su shiga yajin aikin gargadi a ranar 18 ga watan Maris
- Kungiyoyin NASU da SSANU sun sanar da yakin aikin gargadin ne na kwanaki bakwai kan rashin cika masu alkawari
- Wannan na zuwan ne yayin da kungiyar kwadago ta NLC ke barazanar komawa yajin aiki kan halin kunci da ake ciki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyoyin ma'aikatan Jami'o'i na NASU da SSANU za su tsunduma yajin aikin gargadi.
Kungiyoyin sun sanar da yajin aikin ne na kwanaki bakwai daga ranar 18 ga watan Maris kan rike masu albashi.
Menene dalilin shigan NASU, SSANU yajin aiki?
Kungiyar ta tabbatar da shirin shiga yajin aikin ne kan albashin ma'aikatan su da aka rike na watannin hudu, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan shiga yajin aikin da suka yi a shekarar 2022 wanda har zuwa yanzu ba a cika masu alkawuran da aka dauka ba.
Daukar matakin ya biyo bayan ganawa da kungiyoyin biyu suka yi a birnin Akure da ke jihar Ondo a karshen wannan mako, cewar Channels TV.
Gwagwarmayar da kungiyoyin suka yi
Wannan sanarwar yajin aikin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar SSANU, Mohammed Ibrahim ya fitar a yau Litinin 11 ga watan Maris.
A shekarar 2022, watanni biyu bayan shiga yajin aikin ASUU, kungiyoyin biyu sun shiga yajin aiki domin neman hakkinsu a wurin gwamnati.
Kungiyar ta yi korafi kan tsarin rashin biyan kudi idan ba aiki inda ta ce ta bi dukkan tsarin doka kafin shiga yajin aikin, cewar Tribune.
NLC ta bukaci karin albashi
Kun ji cewa Kungiyar Kwadago ta NLC ta bukaci mafi karancin albashi N794, 000 ga ma'aikatan yankin Kudu maso Yamma.
Rahotanni sun tabbatar cewa shugabar kungiyar a yankin, Funmi Sessi ita ya bayyana haka a yau Alhamis 7 ga watan Maris a Legas.
Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki a fadin kasar baki daya.
Asali: Legit.ng