Dole Ma Ta Hakura: Saurayi Ya Yi Sabani da Budurwarsa, Ya Mata Kyautar N1.5m a Matsayin Neman Afuwa

Dole Ma Ta Hakura: Saurayi Ya Yi Sabani da Budurwarsa, Ya Mata Kyautar N1.5m a Matsayin Neman Afuwa

  • Wata ‘yar Najeriya ta nunawa duniya yadda ta kaya da saurayinta da suka samu sabani, ya nemi afuwarta ta manhajar WhatsApp
  • Ta nuna cewa, saurayin nata ya burge ta hanyar tura mata kudi ta bankinta na Opay da UBA, ya tura zunzurutun kudi N1.5m
  • ‘Yan mata da yawa sun yi martani a sashen sharhi, inda suka bayyana mamaki da sha’awar alakar saurayin da budurwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Wata ‘yar Najeriya ta yada bidiyo mai daukar hankali a manhar TikTok, inda ta bayyana yadda ta samu kudi a soyayyarta da sauranyinta.

Ta yada wani hoton tattaunawarsu da saurayin nata ta WhatsApp, inda aka ga saurayin na neman afuwar budurwar.

Kara karanta wannan

Rashin tausayi: 'Yan sanda sun kama wata mata da ta ba diyarta guba

Budurwa ta sha kyautar kudi bayan saurayinta ya bata mata rai
Yadda aka gwangwaje budurwa da kyautar kudi | Hoto: @aurora.jojo
Asali: TikTok

Ya tura mata kudi ta banki

A tattaunawar, saurayin ya bayyana irin kaunar da yake yiwa budurwar fiye da misali. Ya ce ba zai taba bata mata rai da saninsa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bayaninta, ta ce saurayin nata ya mata tsawa ne, inda ta bayyana yadda ta kaya a wani bidiyon da ta yada a shafinta mai suna @aurora.jojo.

Ta nuna hotunan alamar shigan kudi asusunta na banki guda biyu, inda ya zuba N750,000 a kowanne asusu.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a a kafar sada zumunta

Bayan haka ne Legit Hausa ta tattaro kadan daga abin da mutane ke cewa a kasan bidiyon mai daukar hankali. Ga kadan daga ciki:

Deborah:

“Nima fa ina aiki da UBA da Opay. Ya Allah ko dai wannan wata alama ce?”

Jhulee:

“Rabo na da irin wannan soyayyar tun 2021, saurayin da muke soyayya da shi a yanzu shuru ne, babu wata alaka mai karfi.”

Kara karanta wannan

"Sun ce ba zan auru ba": Saurayi ya auri matar da ta haifi yara 4, an yi biki na kece raini

Favour:

“Nima fa ina da Opay, me ya rage kenan.”

Sultan pubg stores:

“Yaro ka tuna fa a soyayya babu bashi, ka bi a hankali.”

Tifeh:

“@ABIKE idan saurayinki ba zai iya rarrashinki a haka ba... ki fada masa ya ba da wuri.”

Tolaniiii:

“Ni ne na ranta masa kudin.”

goddess:

“Cab, lallai zai gane kullum yana rarrashi saboda kullum sai na bata rai.”

blessing Johnson:

“Nima nan ina amfani da Opay da UBA.”

harbeydeymie:

“Yanzu dai irin wannan tuban kadai zan ke karba, ba wai kawai ki yi hakuri na yi laifi ba.”

Yadda saurayi ya raba gari da budurwarsa

A wani labarin, wani mutumi 'dan Najeriya wanda aka fi sani da Josh ya raba gari da sabuwar budurwarsa, Vivian, saboda yadda ta kasa dafa abinci mai dadi.

Wata hirar kafar Whatsapp da ke bayyana yadda suka babe da @JNRdeyforyou ya wallafa a dandalin Twitter ya jawo cece-kuce daga masu amfani da yanar gizo.

Vivian ziyarci Josh a gidansa yayin da ya 'dan fita, inda ta sanar da shi ta WhatsApp yadda ta yanke shawarar girka masa abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel