Daina Kirana Masoyi: Saurayi yayi Watsi da Budurwa Bayan Kwana 1 da Haduwa, Ya Bayyana Dalili

Daina Kirana Masoyi: Saurayi yayi Watsi da Budurwa Bayan Kwana 1 da Haduwa, Ya Bayyana Dalili

  • Wata soyayyar kwana daya ta bare bayan wata hatsaniya tsakanin masoyan guda biyu saboda rashin iya girki
  • Wani mutumi 'dan Najeriya 'dan shekara talatin da doriya ya fusata bayan gano yadda budurwar tasa ta gaza dafa abinci mai dadi
  • Duk da irin hakurin da matar ta yi ta bashi kan cewa za ta nuna bajintarta a gaba, bai sa matashin ya sauya ra'ayinsa na raba soyayya

Wani mutumi 'dan Najeriya wanda aka fi sani da Josh ya raba gari da sabuwar budurwarsa, Vivian, saboda yadda ta kasa dafa abinci mai dadi.

Saurayi da budurwa
Daina Kirana Masoyi: Saurayi yayi Watsi da Budurwa Bayan Kwana 1 da Haduwa, Ya Bayyana Dalili. Hoto daga Twitter/@JNRdeyforyou
Asali: Twitter

Wata hirar kafar Whatsapp da ke bayyana yadda suka babe da @JNRdeyforyou ya wallafa a dandalin Twitter ya jawo cece-kuce daga masu amfani da yanar gizo.

Vivian ziyarci Josh a gidansa yayin da ya 'dan fita, inda ta sanar da shi ta WhatsApp yadda ta yanke shawarar girka masa abinci.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Budurwa Baturiya ta Bayyana Yadda 'Dan Yahoo Ya Karbe Kudin Mahaifiyarta da Soyayya

Vivian wacce ta fara soyayya da Josh na kwana daya ta so burgesa da irin kayataccen abinci amma hakan bai yuwu ba sai ma ya yi sanadiyyar rushewar alakarsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga duban abincin, bayan ta tura kasa hotonshi, Josh ya bukaci su raba gari.

Martanin 'yan soshiyal midiya

@comfort_icewate ta ce:

"Abun haushi, ta yi sadaukarwa. Ita din abun kunya ce ga matan Ibadan. Lallai, ni ina dafa abinci da kyau fa☑️, kada su raina ma ibadan dina wayau fa "

@villageboy01 ya ce:

"Kokari da niyyar ya kamata a duba. Mutum zai iya koyan girki amma ba zai iya koyar soyayya ba ko ya zama natsatstse bayan wasu shekaru ba. Koda ya ke, muna godiya da ka kawo wannan dandalin Twitter."

@Petersonade ya ce:

"Daga ganin rubutun tana da kirki, hali mai kyau, tunani da isashshen ilimi. Duk da irin kalaman cin zarafin da wai shi a dole masoyanta ya mata, ba ta fusata ba, sai ma ta amsa masa cikin sanyin rai. Ita din ba wai yar Ibadan kadai bace, sai dai tana da tushe mai kyau. Ta cancanci a bata dama da agaji."

Kara karanta wannan

Uwa Ta Fasa Asusun Yaranta Bayan Shekaru 10, Ta Fitar Da Tsoffin Kudi a Bidiyo

@jayloveth ta ce:

"Amma ai amala ne kadai da soyayyar ayaba... Kila kubewar bata nuna wa...hakan bai wani yi muni ba."

@murungi_ada ya ce:

"Gaskiya na nishadantu da farkon hirar sai da na kai da sadaukarwan da kuma tsananin shi."

@ddin_i_ ya ce: "

"Na san da hakan! Daga lokacin da ya ce "turomin hoto, na san farkon karshen kenan."

Mai POS ya zage yana hira da mahaukaciya, ya ba jama'a mamaki

A wani labari na daban, wani mai POS ya sha yabo wurin jama'a bayan an gan shi yana shan hira tare da caccafkewa da mahaukaciya.

A wani lokacin cikin har ta kai ga suna neman kai wa juna duka amma suka cigaba da hirarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel