Masu Garkuwa da Mutane Matsorata Ne, Sun Cancanci Hukuncin Kisa, Remi Tinubu Ta Magantu a Bidiyo
- Matar Shugaban kasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta bukaci a yankewa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa
- Ta bayyana hakan ne yayin da take martani kan sace dalibai da malamai 200 a jihar Kaduna da mata 200 a jihar Borno
- Matar Shugaban kasa ta bukaci gwamnoni da ‘yan majalisa da su kawo dokar da za ta tabbatar da hukuncin kisa kan miyagun
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Matar Shugaban kasa Oluremi Tinubu ta bayyana masu garkuwa da mutane a matsayin matsorata.
Ta jaddada cewar ya kamata duk wanda aka kama da wannan laifi ya fuskanci hukuncin kisa.
Wannan martanin na zuwa ne kan lamuran da suka faru a baya-bayan nan, da suka hada da sace mata 200 a jihar Borno da kimanin dalibai da malamai fiye da 280 a jihar Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Duk wanda yake garkuwa da matasa bai da lafiya, mugu ne kuma matsoraci.
“Abin ya isa haka kuma ina kira ga gwamnonin jiha cewa da zarar mun kama su a hannu, sun cancanci hukunci mai tsauri.
“Me zai ka su je ku dauke su daga makarantu? Yanzu, ina ganin abin ya isa haka. A matsayina na tsohuwar ‘yar majalisar tarayya, na yarda cewa duk wanda aka kama cikinsu ya cancanci hukunci mai tsauri.”
- Remi Tinubu
Ga bidiyon a kasa:
Yadda 'yan bindiga suka farmaki makarantar Kaduna
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa an samu tashin hankali a garin Kuriga da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Hakan ya faru ne sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai makarantar firamare ta LEA, Kuriga (1) tare da sace dalibai da dama.
An gano yawan yaran da aka sace a Kaduna
A halin da ake ciki, mun ji cewa shugaban makarantar firamare ta LEA da ke Kuriga a karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, Sani Abdullahi ya tabbatar da cewa dalibai 287 na makarantar ne wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su.
Mallam Abdullahi na daga cikin wadanda 'yan bindigar suka yi awon gaba da shi amma daga baya ya tsere tare da wasu dalibai.
Shugaban makaranta ya ba da labarin yadda 'yan bindiga suka sace dalibai 287 a Kaduna.
Asali: Legit.ng