Mayakan Boko Haram sun sake kwashe matan aure da 'yan mata a Borno

Mayakan Boko Haram sun sake kwashe matan aure da 'yan mata a Borno

- A daren Juma'a, wurin karfe 11 na dare ne mayakan ta'addancin Boko Haram suka sake kwashe matan aure da 'yan mata a Borno

- 'Yan ta'addan sun yi awon gaba da kayan abinci da Shanu a cikin sa'o'i biyu da suka kwashe suna aika-aikar

- Sun kai harin ne kauyen Mahalaram da ke da nisan kilomita kadan daga Damboa amma kilomita 87 tsakaninta da Maiduguri

Mayakan ta'addancin Boko Haram sun yi garkuwa da mata manya tare da kanana yayin wani hari da suka kai Borno, jaridar Sun News ta ruwaito.

Harin ya faru ne a daren Juma'a yayin da 'yan ta'addan suka kai hari Malaharam da ke karamar hukumar Biu wurin karfe 11 na dare, mijiya daga jami'an tsaro ta tabbatar.

Malaharam na da nisan kilomita kalilan daga Damboa amma kuma kilomita 87 tsakaninta da Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

'Yan ta'addan sun yi awon gaba da kayan abinci tare da Shanu kuma sun kwashe wurin sa'o'i biyu suna aika-aika a kauyen, wani dan uwan daya daga cikin matan da aka yi garkuwa da su ya sanar da The Sun.

Mayakan Boko Haram sun sake kwashe matan aure da 'yan mata a Borno
Mayakan Boko Haram sun sake kwashe matan aure da 'yan mata a Borno. Hoto daga HumAngle
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda Dino Melaye ya rera wakar 'ba'a' ga Oshiomhole

A wani labari na daban, an damke wani sojan Najeriya da ya yi wa shugaban rundunar sojin Najeriya da sauran shugabannin tsaro kaca-kaca a wani bidiyo.

A wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani, sojan mai mukamin Lance Corporal mai suna Martins, ya zargi shugaban rundunar sojin najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai da sauran shugabbanin kasar nan da rashin kokari.

Ya zargesu da nuna halin ko in kula a kan kashe-kashen da ke faruwa a sassan kasar nan. Ya ce 'yan bindiga da mayakan ta'addancin Boko Haram na cin karensu babu babbaka.

A bidiyon mai tsawo, Lance Corporal Martins ya ce shugabannin tsaron Najeriya sun gaza. Ya kushe shugabannin tsaron Najeriya ballantana Buratai da shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Abayomi Gabriel Olonisakin, a kan yadda ake ci gaba da kashe-kashe.

Ya zargi cewa rundunar sojin ta bada umarnin tsare wasu dakarun wadanda suka bukaci makamai na zamani don yakar Boko Haram da sauran 'yan ta'adda a kasar nan.

Ya tabbatar da cewa akwai yuwuwar a kama shi ko kuma a kashesa saboda wannan bidiyon amma ya ce ya sadaukar da kansa ga kasarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: