Lafiya Jari: Ɓarkewar Cuta Ta Jawowa Makarantu Tafiya Hutun Dole, An Ɗauki Mataki a Jihar

Lafiya Jari: Ɓarkewar Cuta Ta Jawowa Makarantu Tafiya Hutun Dole, An Ɗauki Mataki a Jihar

  • Gwamnatin jihar Kuros Riba ta tabbatar da ɓarkewar cutar kyanda a wasu makarantu biyu a ƙaramar hukumar Akpabuyo
  • Rahoto ya nuna cewa bullar cutar ta tilastawa makarantun tafiya hutun dole yayin da gwamnati ta fara yunƙurin kawar da ciwon
  • Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Henry Ayuk, ya ce an ci gaba da rigakafin cutar kyanda domin kare yara daga shiga matsala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kuros Riba - An samu rahoton bullar cutar kyanda kuma an tabbatar da ita a wasu makarantu biyu da ke cikin karamar hukumar Akpabuyo ta jihar Kuros Riba.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Henry Ayuk, ya tabbatar da ɓarkewar cutar, ya jero sunayen makarantun waɗanda suka haɗa da makarantar sakandiren sojojin ruwa da Penniel Primary School.

Kara karanta wannan

"Saura ƙiris ku ji daɗi" Shugaba Tinubu ya aika saƙo ga ƴan Najeriya, ya kaddamar da sabon shiri

Gwamnan jihar Kuros Riba, Bassey Otu.
Barkewar Cutar Kyanda Ta Kawo Babban Cikas a Wasu Makarantu a Jihar Cross River Hoto: Sanator Prince Bassey Otu
Asali: Facebook

Ya ce tuni suka tashi tawagar kai agajin gaggawa ta ma'aikatar lafiya a jihar Kuros Riba kuma an tura su zuwa yankin domin shawo kan cutar, The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki gwamnati ta ɗauka?

Bugu da ƙari kwamishinan ya ce, “an dawo da allurar rigakafi ga yara a yankunan da abin ya shafa da kuma sauran kananan hukumomin da ba a samu rahoton bullar cutar ba."

Ya ce hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta jiha ta kara matsa kaimi wajen rigakafin yau da kullum domin jama'a su samu kariya daga kamuwa da cututtuka.

Dakta Ayuk ya yi gargaɗi cewa cutar kyanda cuta ce mai saurin yaɗuwa, musamman a tsakanin yaran da ba a yi musu rigakafi ba.

Bisa haka ya yi kira ga iyaye tare da ƙarfafa musu guiwa su kai ƴaƴansu wuraren rigafin wannan cuta domin kare su daga haɗarin kamuwa da ita.

Kara karanta wannan

Majalisa ta buƙaci Shugaba Tinubu ya gaggauta kawo ƙarshen ƴan bindiga a Jihar Arewa

An kulle makaranta saboda cutar kyanda

Tuni dai mahukuntan makarantar sakandiren sojojin ruwa suka rufe makarantar sakamakon barkewar cutar tare da umurtan iyaye su gaggauta zuwa su dauki ‘ya’yansu.

Kokarin jin ta bakin kwamandan makarantar, Kyaftin FI Uchieme bai yi nasara ba saboda lambar wayarsa ba ta shiga ba, rahoton Politics Nigeria.

Shugaban kungiyar iyayen yara a makarantar, Okon Bassey, ya tabbatar da samun sakon da ya tilasta wa yaransu tafiya hutu saboda cutar.

An kama ɗaliban da suka kashe abokinsu

A wani rahoton kuma wasu dalibai hudu da ba a bayyana sunayensu ga manema labarai ba sun kashe abokin karatunsu ta hanyar lakada masa duka.

Rahotanni sun ce dalibin ya gamu da ajalinsa ne bayan da abokan hudu suka kama shi yana nadar bidiyon su, lamarin da ya ja suka duke shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel